✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban ce za mu kayyade haihuwa ba – Ministar Kudi

Bayan ’yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu kan kalaman da wasu kafofin watsa labarai suka ruwaito cewa, Minsitar Kudi Hajiya Zainab Ahmed ta yi game…

Bayan ’yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu kan kalaman da wasu kafofin watsa labarai suka ruwaito cewa, Minsitar Kudi Hajiya Zainab Ahmed ta yi game da batun kayyade iyali, Ministar ta musanta cewa ta ce gwamnati za ta kayyade wa mata ’ya’yan da za su rika haihuwa.

A shekaranjiya Laraba ce jaridar Punch ta ruwaito cewa Ministar ta ce “Gwamnatin Tarayya na shirin kayyade yawan yaran da kowace mace za ta haifa a kasar nan.”

Jaridar ta ce Zainab Ahmed ta fadi haka ne a yayin wani taro kan tattalin arziki a Abuja, Babban Birnin Tarayya.

Jaridar ta ruwaito Zainab Ahmed tana cewa: “Kuma muna fata da goyon bayan sarakunan gargajiya da malaman addini, za mu kai gabar da za mu iya samar da wani tsari da zai kayyade wa mata yawan yaran da za su iya haifa, saboda hakan yana da muhimmanci wajen dorewar ci gabanmu.”

Sai dai sa’o’i kadan bayan fitowar labarin ne, sai Ministar ta wallafa wani sako a shafinta na Twitter da ke cewa “Ba mu taba cewa za mu sa dokar kayyade iyali ba.” Kamar yadda BBC ya ruwaito daga shafin nata.

Sakon na Ministar ya kara da cewa: “Gwamnatin Tarayya tana  ganawa da masu ruwa-da-tsaki kamar sarakunan gargajiya da malaman addini don su bai wa mabiyansu shawara a kan ba da tazarar haihuwa. Amma ba mu taba cewa za mu sa doka kan kayyade iyali ba.”

“Me ake nufi da tazarar haihuwa? Wannan wani abu ne da ke da muhimmanci wajen lafiyar mata, a rika samun tazara tsakanin haihuwa,” inji ta.