Wadansu ma’aurata ’yan asalin kasar Birtaniya, sun samu shiga Kundin Tarihi na Duniya (Guinness World Records), sakamakon kasancewarsu ma’auratan mafi girman bambancin tsawo a tsakaninsu.
Bayanai sun ce matar ta fi mijinta tsawo da kafa biyu.
Alkaluman sun nuna cewa, wannan shi ne ne mafi girman bambancin tazara da aka taba samu a tsakanin ma’aurata.
Ma’auratan James da Chloe Lusted, sun yi aure ne a 2016, kuma an ba su lambar Guinness saboda tsawo.
Bayan auna tsawonsu, an samu James yana da tsawon kafa 3 da inci 7, ita kuma Chloe Lusted tana da tsawon kafa 5 da inci 5.
James Lusted mai shekara 33, wanda dan wasan kwaikwayo ne kuma mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin, ya hadu da Chloe mai shekara 27, wadda malama ce ta hanyar abokai a shekarar 2012.
An haifi James da cutar da take hana girma da sa gajartar a gabbai (diastrophic dysplasia) wadda take mayar da mutum ya zama wada.
“Labarinmu na soyayya ya koyar da mu kuma ya koyar da wadansu cewa, ba za ku iya yi wa abu hukunci ba nan take, kawai ku so mutum kowace irin halitta take gare shi.
“Ba na tsammanin za ku iya zaben wanda bai mamaye zukatanku da so ba,” inji Chloe Lusted.