Assalamu Alaikum, barkanmu da Sallah, Allah Ya amshi dukkanin ibadunmu kuma Allah Ya sa a yi shagalin Sallah lafiya, amin. Ga bayani akan abubuwan da ma’aurata za su aikata don tafiyar da bambanci sha’awa a tsakaninsu, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, ya kuma haifar da karuwar farin ciki da jin dadi cikin rayuwar aurensu, amin.
Hanya Ta 1 : Maigida ya zama cikakken namiji:
Maigida, ya fahimci cewa shi ne maigidan, shi ke jan ragamar gidan, da uwargidan da gidan duk karkashinsa suke. Komai irin murdewar halayyar uwargida ko irin nauyin sha’awarta, in maigida ya gane sirrin da ke cikin aiwatar da dukkan fasahohi da kuzarorin namijintakarsa, to zai iya tafiyar da uwargidarsa yadda yake so kuma zai iya zuko da daskararriyar sha’awar ta waje. Ba macen da ba ta da sha’awa, sai dai dole akwai wasu mabudai da ake amfani da su don bankado da sha’awarta daga cikin jikin ta har ta bayyana. Ga magidanta da ke ganin kamar matayensu ba su da sha’awa to mabudan da suke amfani da su ba su yi daidai da irin kofofin sha’awar matayen nasu ba shi ya sa.
Zama cikakken namiji ba wai kawai a yi ta ji da mace ba ne ta hanyar yi mata duk abin da take so da guje wa abubuwan da ba ta so, zama cikakken namiji shi ne amfani da wannan karfin hankali, karfin hangen nesan da karfin kuzarin nan da Allah SWT ya ba maza sama da mata wajen aiwatar da kowane bangare na rayuwar aure.
Mace na jin dadi da samun kwanciyar hankali in har ta tabbatar da cewa mijinta cikakken namiji ne ta kowane bangare na rayuwa, wannan jin dadi da kwanciyar hankalin kuwa shi ne mabudin babbar kofar sha’awar ’ya mace.
Sannan mu tuna da fadin Manzon mu (Sallallahu Alaihi Wasallam) ga Magidanta: “Mafi alherin cikinku su ne mafiya kyautatawa ga matayen su” don haka magidanta masu sa tsauraran matakai ga matayensu da ka’idoji masu takurawa ga matansu to ku sani namijintakar ku ta yi rauni saboda haka sai ku gyara halayenku.
Abu ma fi dacewa shi ne fahimtar uwargida da fahimtar yanayin halayyarta sai a sa mata dokoki daidai da ita, duk wata dokar da za ka sa wa matarka, komai alfanun ta, in dai wannan doka ta zama mai tsananin takurawace gareta, to fa a hankali son ka zai ta raguwa cikin zuciyarta, ga yanayin halayyar ‘ya mace kuwa, in ba so to ba sha’awa!
Hanya Ta 2: Uwargida ta zama cikakkiyar mace:
Ga duk Uwargidan da take son samun nasara da farin ciki a gidan aurenta, a duniyarta da kuma lahirar ta, to dole sai ta zama cikakkiyar ’ya mace, ta hanyar bankado da dukkanin siffofi, halayya da dabi’un macentaka da Allah (SWT) Ya gina jiki da ruhin ’ya mace da su. In Uwarguda ta rika jin tana da wani nakasu a fannin cikar macentakarta, to wannan zai dakusar mata da sha’awarta, mace ta fi jin sha’awa in ta rika jin ita cikakkiyar mace ce ta ko’ina, shi ya sa zaka mazan da suka gane wannan sirri suna yawan yaba wa hikimomin macentakar matansu kusan kowane lokaci.
Kowace mace akwai wata irin baiwa ta musamman da Allah (SWT) Ya yi mata, matsalar yawancin mata ba su san irin baiwarsu ba balle su san yadda za su sarrafata har ta amfanar da rayuwar aurensu. Don haka yana da kyau uwargida ta yi kokari ta fahimci kanta da yanayin halayyarta, domin ta san yadda za ta rika sarrafa hikimomin macentakarta don samun babbar nasarar rayuwar aure.
Ado da kwalliya muhimmai ne daga cikin dabi’un jinsin ’ya mace da yin su ke rayar da sha’awarta, don haka yana da matukar alfanu ga uwargida ta kasance kodayaushe cikin kwalliya, ba wai lallai sai lokacin tarbar maigida ba, har ma da lokacin gabatar da aikace-aikacen gida, ya kasance kodayaushe ta yi kwalliyar ta daidai gwargwado, da ’yan kunne, sarka, warwaro da duk wani abun makalawa na kwalliya a jikinta, domin wannan zai kara fito wa uwargida da kwarjinin macentakarta, wanda ya kan taimaka wajen ji da motso da sha’awar ’ya mace, kuma ya samar mata wadatar zuci.
Sai sati na gaba ci gaban bayanin na zuwa insha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.