✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bambance-bambancen da ke tsakanin mace da namiji

A Duk lokacin da ake magana a kan bambanci tsakanain namiji da mace, to ana magane ne a kan bambancin da tsarin halitta ya haifar…

A Duk lokacin da ake magana a kan bambanci tsakanain namiji da mace, to ana magane ne a kan bambancin da tsarin halitta ya haifar ba wai don wani jinsin ya fi wani jinsin ba, halitta ce ta samar da haka, wannan ne ya sa suke zama tare, ba tare da sun gaji da juna ba, kuma halittarsa ce ta dora wa kowane nauyin da ya fi dacewa da shi. 

Don haka, ga abin da masana halayyar dan Adam, da malamai, da kuma likitoci suka bayyana dangane da bambancin da ke tsakaninsu don a fahimci yanayinsu da kuma irin rawar da kowanensu zai iya takawa a rayuwarmu ta yau da kullum.
TSARIN HALITTA:Idan muka dauki girman jiki da tsawo, mafi yawa mata kananan jiki ne da su, maza kuma sun fi girman jiki, yawancin mata gajeru ne a kan maza. Sautin muryar namiji yana da girma, ita kuma mace muryarta siririya ce, mace ta fi namiji saurin girma, domin tun tana cikin mahaifa , mace ta fi garkuwar kamuwa da cututtuka, haka nan mace tana riga namiji saurin balaga, kuma tana riga namiji daina haihuwa. Huhun namiji ya fi na mace zukar iska. Haka nan ita kanta kwakwalwa ta namiji ta fi ta mace zukar iska. Haka nan ita kanta kwakwalwar namiji ta fi ta mace girma. Zuciyar namiji ta fi saurin bugawa a kan ta mace.
HALAYYA: A halayyar kuma masana sun yi amanna cewa, namaiji ya fi mace son aikin karfi, da gwagwarmaya, mace kuwa ta fi son tafiyar da komai a hankali. Mace ba ta iya yanke shawara a gurguje, kamar yadda namiji kan yanke nan take. Wannan dalili ne ya sa da wuya ka ji mace ta rataye kanta, ita ta gwammace ta sha guba, ko wani magani da zai hallaka ta nan take wanda bai taka kara ya karya ba, shi kuwa namiji hakan bai zama abin a zo a gani a wajensa ba.
Mace ta fi son kwalliya da duk wani abin da zai kayatar da ita, fiye da namiji.Haka nan mace ta fi namiji surutu, kuma ta fi namiji kula da yara, ita hankalinta a kullum a kan ci gaban iyali ya ke.Kuma ita mace ba ta iya boye sirri kamar yadda namiji yake boyewa. Mace ta fi namiji saurin kuka, ta yadda za ka ga cewa abu kadan zai iya sanya mace kuka.
ZAMANTAKEWA: Masana sun ci gaba da cewa sha’awa ce ke sa namiji son mace, amma shi namiji muhimmancinsa ne ke sa mace sonsa.Burin namiji shi ne ya samu macen da zai iya iko da ita, ita kuwa a kullum so take ta samu mai kaunarta.Mace ta fi son ganin jaruntar namiji, shi kuwa kwalliya da kyawun mace su ne a gabansa. Duk matsayin da mace take ciki tana iya boye son jima’i fiye da namiji.
Bincike ya tabbatar da cewa da a ce mace tana da kamanni irin na namiji da halayya irin ta sa, da ba za ta iya ba shi sha’war da zai ja ta gare shi ba, ballantana ma har su iya zama tare su yi mu’amala irin ta auratayya tare.
Na binciko wadannan bambance-bambance ne don a fahimci yanayin kowa da kuma irin rawar da kowanensu zai iya takawa, saura da me? Allah subhanahu wata’ala yana cewa a cikin alkur’ani “Ba mu halicci mutum da aljani ba sai don su bauta min.” Ka ga ke nan, akwai matukar bukatar mu kyautata alakar da ke tsakanin namiji da mace, musamman ma a zamantakewar aure.Domin gyaruwarta shi ne gyaruwar al’umma, Allah ya agaza mana.
Za a iya samun Ibrahim Hamisu a 080 60651676
Email: [email protected]