✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bam ya tashi a gidan kallon kwallo a Yobe

Da yawa daga cikin mutanen da suka halarci gidan kallon kwallon Jamilu Cross Fire Football biewing Centre da ke Damaturu ne suka rasa ransu bayan…

Da yawa daga cikin mutanen da suka halarci gidan kallon kwallon Jamilu Cross Fire Football biewing Centre da ke Damaturu ne suka rasa ransu bayan da wani bam da aka dasa a Keke-Napep ya tashi a ranar Talatar da ta gabata da misalin karfe 8 da minti 9 na dare watau a daidai lokacin da ake kallon wasa a tsakanin kasashen Brazil da Meziko a gasar cin kofin duniya da yanzu haka take gudana a Brazil.
Wani wanda ya tsallake rijiya da baya ya ce bam din ya tashi ne daga wani Keke-Napep da aka ajiye a kusa da wurin.
“Ba mu ankara ba sai muka ji wata irin kara, kafin ka ce kwabo wuta ta kama kuma daukacin wurin ya turnuke da hayaki.  Ni dai na yi sa’ar tsallake katangar da ke zagaye da wurin inda na ranta cikin na kare kuma Allah kadai Ya san yawan mutanen da abin ya rutsa da su”, inji shi.
Kwamishinna ’yan sandan Jihar Yobe Marcus danladi ya tabbatar da aukuwar wannan lamari.
Idan za a tuna, Hedkwatar rundunar tsaro ta sojoji ta gargadi jama’a da su daina zuwa gidajen kallon kwallo a lokacin gasar cin kofin duniya saboda matsalar masu kai hare-hare a irin wadannan wurare.
A makwannin da suka wuce bam ya tashi a gidan kallon kwallo a Adamawa inda ya kashe mutane da kuma jikkata wasu da dama.
Haka abin ya kasance a garuruwan Jos da Borno da hakan ta sa gidajen kallon kwallo suka dauki matakan matsaro a lokacin da ake nuna gasar cin kofin duniya da yanzu haka ke gudana a Brazil.