Wata mota makare da bama-bamai da ‘yan ta’addar kungiyar ISWAP suka tayar ta kashe sojoji uku a jihar Borno.
Wasu sojoji 10 kuma sun samu rauni a harin na ranar 14 ga Mayu, 2023, a yayin da sojojin suke ci gaba da kai samame kan sansanin ISWAP da ke yankin Tunbum Reza.
- Zargin batanci: Kotu ta ba da belin Dokta Idris Abdulaziz
- Abin da Kwankwaso da Tinubu suka tattauna a kasar waje
Wani kwararre a fannin yaki da tada kayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce sojojin sun mayar da martani inda suka kashe ’yan ta’addan da dama.
A cewarsa, motar da ke makare da bam din ta ci karo ne da wata mota yaki ta sojojin Najeriya, wadda wata motar kirar Hilux ke biye da ita.
Wata majiyar soji a Maiduguri ta ce ‘yan ta’addan sun yi asarar dimbin mayaka, duk da cewa ba a tabbatar da adadinsu ba ya zuwa yanzu.
Makama ya ce: “Wannan harin ya zo ne kasa da sa’o’i 24 bayan sojoji sun dakile wani hari a Arege, inda kashe ‘yan ta’adda 10 tare da lalata motocinsu uku.
“Sun yi wani gagarumin yunƙuri na kutsa wa sojojin da ke gaba ta hanyar amfani da bama-bamai da aka tayar da su a cikin mota, amma nan take aka kashe su.”
Ya kara da cewa, an kwashi dakarun da suka samu raunuka zuwa wani asibitin sojoji da ke Maiduguri domin yi musu magani.