Wani abin fashewa da ake kyautata zaton bam ne ya tarwatse a wata gadar da mutane ke bi a birnin Istanbul na kasar Turkiyya, inda ya hallaka mutum hudu, wasu 38 kuma suka jikkata.
Bam din ya tashi ne a kan gadar da ke kan titin Istiklal a unguwar Taksim, da misalin karfe 4:20 na yammacin Lahadi, wato misalin karfe 2:20 a agogon Najeriya.
- Jiragen yakin Amurka 2 sun yi taho-mu-gama a sararin samaniya
- Zanga-zangar tsadar rayuwa ta ci rai a Albaniya
Wasu hotunan inda lamarin ya faru sun nuna yadda motocin daukar marasa lafiya da na kashe gobara da kuma na ’yan sanda ke ta kokarin aikin ceto a wajen.
Har zuwa yanzu dai ba a kai ga gano musabbabin fashewar ba.
Wakiliyar gidan talabijin na Aljazeera a Istanbul, Sinem Koseoglu, ta ce ana zargin fashewar ba za ta rasa nasaba da kunar bakin wake ba, kodayake har yanzu babu wata sanarwa a hukumance a ka hakan.
Sinem ta kuma ce harin ya zo wa mutane da dama da ba-zata, sakamakon babu wani gargadi gabanin hakan kan barazanar kai hari.
Sai dai ta ce an tsaurara matakan tsaro matuka a yankin. (Aljazeera)