✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Balotelli ya sayi motar Naira miliyan 65

Shahararren dan kwallon kulob din AC Milan da ke Italiya da ke  shawa’ar yin hulda da abubuwa masu tsada kamar zobe da sarka da dan…

Sabuwar motar da Mario Balotellil ya saya ta Naira Miliyan 65Shahararren dan kwallon kulob din AC Milan da ke Italiya da ke  shawa’ar yin hulda da abubuwa masu tsada kamar zobe da sarka da dan kunne da agogo da mota da sauransu, a karshen makon jiya ne ya sayi sabuwar mota da kudinta ya kai Naira miliyan 65.
Motar, kirar F12 Ferrari an kiyatsa kudinta ne a kan Fam dubu 250 kwatankwacin Naira miliyan 65.
Rahotanni sun tabbatar dan kwallon ya mallaki motoci fiye da biyar masu tsada da suka hada da Audi R8 da Maserati GT da Bentley Continental GT da Ferrari 458 da Spider da Range Rober Ebokue da kuma wacce ya saya yanzu Ferrari F12.
An ga dan kwallon da sabuwar motarsa yana yawo a cikin garin Milan a lokacin da ya tsaya a kantin Louis buitton ya yi sayayya tare da wani abokinsa.