✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bakuwar dabba ta kashe raguna 6 a Abaji

Jama’ar Unguwar Sokodabo a karamar hukumar Abaji da ke babban birnin tarayya Abuja sun fada cikin fargaba bayan wata bakuwar dabba ta kashe raguna 6…

Jama’ar Unguwar Sokodabo a karamar hukumar Abaji da ke babban birnin tarayya Abuja sun fada cikin fargaba bayan wata bakuwar dabba ta kashe raguna 6 a unguwar.

Wani mazaunin unguwar Aliyu Usman ya bayyana cewa, ragunan an killace su ne a wajen da ake kiwon su, bayan wayewar gari sai mai ragunan ya tashi samu ragunan duk a mace.

Aliyu Usman ya ce, dabbar da ake zargi da kashe ragunan ta jiwa ragunan rauni ta hanyar shan jinin su. Wakilinmu da ya ziyarci unguwar ya samuragunan a mace kuma hanjin ragunan a waje.