A yau mun wayi gari da wata bakuwar al’ada da ta bayyana a cikin al’umma mai suna ‘yancin mata wadda da yawa mata ‘yan Boko sun kakkafa kungiyoyi da assasa su domin su yi tasiri a zukatan ‘yan’uwansu mata da sunan wakar ‘yanci wanda hakika idan ba mu yi taka tsantsan ba to a karshe tarbiyar da akasan al’ummar Musulmi da ita to za ta rushe domin a kullum kungiyoyi sai kara karfafa suke yi da manufofin cewa wai lokaci ya yi da ya kamata a ce mata sun ‘yantu daga kangi na bauta, danniya da kuma tursasawa.
Idan kuma muka dubi wannan kalmar ta ‘yanci a mahangar addini to za mu ga cewa shi addinin Musulunci ya girmama mace kuma ya ba ta ‘yanci mai yawa fiye da duk wani addini. Misali, tun da farko idan muka duba za mu ga cewar da can a lokacin Jahiliyya mace ba ta samun gado domin ita kanta ma kayan gado ce, mace ba ta da ikon zabar wa kanta miji kuma ba ta da ‘yancin zama a gidan miji ta huta irin na aure ya zama dole ta tashi ta nemi abin da zat a ci da kanta da iyalinta, ba su da ikon su yi doguwar rayuwa. Domin kuwa idan mutum aka haifa masa ‘ya mace sai ya ji kamar an haifa masa abin kunya don haka sai ya je ya binne ta da ranta ko ya rataye ta. Amma da Musulunci ya bayyana sai ya ba su cikakken ‘yanci wanda ba su da shi ada.
Misali Musulunci ya hana a rika karkashe su kana ya ba su ‘yancin samun gado: Alkur’ani ya zo da umurnin cewa lallai ne a raba gado tare da su kuma ya haramta a sanya su a cikin kayan gado, sannan Musulunci ya ba su ‘yancin zaben miji. Manzon Allah (SAW) ya yi umurnin cewar kada a aurar da mace har sai da izininta (bazawara ta kan yi furuci da kanta a kan zaben miji amma budurwa ka ta kan yi shiru domin sh ine alamar izininta). Haka kuma Musulunci ya hana a rika bautar da su ya kuma yi umurni da a girmamasu, a kyautata musu.
Haba yan’uwa mata ku dubi fa masu bin addinin Hindu ko addinin Kirista idan mazajensu suka mutu to shike nan ba su ba sake yin aure har abada.Sai dai su zauna haka har mutuwarsu ko kuma su yi ta sheke ayarsu da ‘ya’yan cikinsu ko kuma da ‘yan uwan mijin amma da Musulunci ya ba da damar mace ta sake yin aure bayan wata hudu da kwana goma da rasuwar mijinta. Ya ke ‘yar uwata hakika ‘yancin mata a Musulunci ba zai lissafu ba.
Shin wane irin ’yanci ne Musulunci bai ba ku ba da har za ku kakkafa kungiyoyin kare ’yancin mata? Ku sani a Turai sai a tsakiyar karni na 20 suka samu ’yancin yin walwala da kubuta daga bauta daga hannun
mazajensu,haka zalika su fa a Turawa ai dabara da wayo suka y iwa mata a yayin da suka bullo musu da manufofin da ta kai su ga tunanin samun ‘yanci daga danniya amma fa a fakaice mazajen sun yi haka ne domin su samu saukin gudanar da
al’amuran rayuwa da kuma yin taimakekeniya wajen aikin ofis da sh’anin gida.
Ku kuwa Musulunci ya ba ku ’yanci tun sama da shekara dubu da suka wuce, don haka ’yan uwana mata kada ku yarda da duk wata farfaganda a kan neman ’yanci, domin a zahiri Turai suna amfani da kalmar neman ’yanci ga al’ummar Musulmi domin su ruguza kyakkyawar tarbiyyar da muka samu a Musulunci kuma makamin da suke amfani da shi na farfaganda ya fi makamin nukiliya barna domin zai iya ragargaza koyarwar addinin Musulunci, wanda kafin mu farga mu gyara tuni mun makara.
A karshe ina fata ’yan uwana mata za su yi hattara .
Daga Ado Musa Unguwar kaura Goje Kano 08069186916