✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bakin haure 76 sun rasu bayan kwalekwalensu ya yi hatsari

Ana aikin ceto domin wanda suka bace sakamakon hatsarin a gabar Tekun Mediterranean da ke kasar Siriya Siriya

Bakin haure 76 sun mutu bayan kwalekwalen da suke ciki ya nutse a gabar Tekun Mediterranean a kasar Syria.

Gwamnatin Kasar Siriya ta ce kimanin mutum 150 ne ke cikin jirgin ruwan bakin hauren a lokacin da abin ya faru, kuma 20 daga cikin fasinjojin kawai aka tabbatar da sun tsira da ransu.

Ma’aikatar Sufuri ta kasar Siriya ta bayyana cewa ana ci gaba da aikin ceto domin gano wadanda suka bace sakamakon hatsarin.

Ya ce akwai kananan yara akalla 45 a cikin kwalekwalen kuma akasarin bakin hauren sun taso ne daga makwabciyarsu, Lebanon.

Adadin wadanda suka rasu a hastarin shi ne mafi girma a hadurrann jirgin ruwa mai dauke da bakin haure daga Lebanon a ’yan shekarun nan.

Kasar Lebanon da ke karbar ’yan gudun hijira sama da miliyan daya da suka tserewa yakin basasar Siriya, ta fada cikin matsalar tattalin arziki tun shekar 2019.

Kasar na zama a matsayin zango ga bakin haure, wadanda ke yin tafiyar kasa ba bisa ka’ida ba zuwa kasashen Turai a cikin jiragen ruwa masu daukar mutane fiye da kima.

Matsalar tattalin arzikin Lebanon ta haifar da karuwar mutanen da ke yunkurin ficewa daga kasar zuwa wasu wurare.

Shekaru uku ke nan da Lebanon ta fada cikin matsalar tattalin arziki, wadda Bankin Duniya ya ayyana a matsayi mafi muni a wannan zamani.

A 2021 Bankin Duniya ya sanar cewa an samu karuwar bakin haure masu yin irin wannan tafiyar kasada daga Lebanon.