✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bajimba: Garin da ake debar ruwa a rijiya daga karfe 12 na dare zuwa 6 na safe

Al’ummar kauyen Bajimba da ke Karamar Hukumar Gassol a Jihar Taraba na fuskantar matsalar rashin ruwan sha tare da sauran ababen more rayuwa. Mazauna garin…

Al’ummar kauyen Bajimba da ke Karamar Hukumar Gassol a Jihar Taraba na fuskantar matsalar rashin ruwan sha tare da sauran ababen more rayuwa.

Mazauna garin sun dogara ne a kan wata rijiya daya kacal da ke garin wajen samun ruwan sha da sauran aikace-aikacen yau da kullum.

Aminiya ta samu labari cewa daga karfe 12 na dare zuwa karfe 6 na safe ake dibar ruwa a rijiyar a kullum, kamar yadda wakilin Aminiya ya jiyo a kauyen.

Mai unguwar kauyen, Mista James Dauda ya shaida wa Aminiya cewa saboda a samu ruwa mai yawa ne aka tsara lokacin dibar ruwa a rijiyar daga karfe 12 na dare zuwa karfe 6 na safe a kullum.

Ya ce wannan tsari ya zama tilas domin yawan masu bukatar ruwa a kauyen ya fi ruwan da za a iya samu a rijiyar.

Mista James Dauda ya ce daga bayan karfe 6 na safe ba wanda zai sake dibar ruwa a rijiyar sai kuma karfe 12 na dare domin ta haka ne kawai ruwa mai yawa zai sake taruwa a rijiyar.

Mai unguwar ya kara da cewa akwai rijiyar burtsatse daya a kauyen amma tuni ta lalace kuma sun nemi a gyara musu amma har yanzu bai yiwu ba.

Mai unguwar ya ce bayan matsalar ruwan sha akwai matsalar rashin hanyar mota a yankin. Ya ce mazauna kauyen tare da sauran al’ummar wasu kauyuka da ke makwabataka da su na shan wahalar zirga-zirga zuwa hedkwatar Karamar Hukumar da ke garin Mutum Biyu da kuma zuwa kasuwanni don kai kayan gona.

Ya ce matsalar ta fi muni da damina inda ruwa ke yanke hanyarsu a wurare daban-daban zuwa babban titin Jalingo zuwa Wukari.

Mai unguwa James ya ce a yankin ba su da dakin shan magani wanda hakan ke haifar da matsala wajen daukar marasa lafiya zuwa garin Jalingo ko kuma garin Mutum Biyu don a yi musu jinya.

Ya nemi Karamar Hukumar Gassol da Gwamnatin Jihar Taraba su kawo wa al’ummar yankin dauki ta fuskar samar musu da ababen more rayuwa.