Iyalan fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna 62 da aka sace tsawon kwanaki 42 da suka wuce, sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da dawo da sufurin jirgin kasan har sai an kubutar da ‘yan uwansu da ‘yan bindiga suka yi awon gaba da su.
Wasu daga cikin iyalan wadanda aka sace a jirgin kasan sun gudanar zanga-zanga a titunan Jihar Kaduna, don nuna damuwarsu kan rashin ceto ‘yan uwansu.
- Mazauna sun firgita da ganin makwabci a cikin ’yan bindigar da suka kai musu hari
- Wahalar man fetur ta sake kunno kai a Abuja
Haka kuma an samu wasu daga cikinsu da suka gudanar da ta su zanga-zangar a Abuja, babban birnin Najeriya.
Aminiya ta rawaito yadda maharan a ranar 28 ga watan Maris, 2022 suka dasa bam a titin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, wanda ya yi sanadin lalata jirgin tare da raunata mutane da dama, baya ga wadanda maharan suka harbe sannan suka sace.
Maharan sun kashe mutum tara a cikin jirgin sannan suka sace mutum 60, kafin daga bisani suka saki Manajan-Daraktan Bankin Noma, Alwan Ali Hassan.
Hukumar Sufurin Jiragen Kasa (NRC), ya bayyana cewar an kammala gyaran titin jirgin da maharan suka lalata, sai dai kamfanin bai bayyana lokacin da zai dawo bakin aiki ba.
Kazalika, cikin wata sanarwa da iyalan wanda aka sace suka fitar a ranar Litinin a Kaduna, sun bukaci da a dakatar da dawowar sufurin jirgin kasan har sai an tabbatar da kubutar ‘yan uwansu.
Da ya ke magana, mai magana da yawun iyalan, Dokta Abdulfatai Jimoh, ya ce Hukumar Sufurin Jiragen Kasan ta yi biris da umarnin shugaba Buhari, na yi musu karin haske kan abubuwan da ke faruwa game da iyalansu.
Shugaba Buhari ya gana da iyalan wadanda aka sace lokacin bikin sallah, inda ya bai wa Hukumar NRC umarnin kafa kwamitin da zai ke bai wa iyalan bayanai game da halin da ake ciki kan sace ‘yan uwansu.
“Mako guda ke nan da shugaban kasa ya bada umarni, amma har yanzu NRC ba su tuntubi iyalan wadanda aka sace ba. Irin wannan hali na ko in kula na bukatar hukunci,” a cewar Jimoh.