✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bai kamata a rika sanya siyasa a matsalar tsaron Najeriya ba – Musallah

  Alhaji Sadik Ibrahim Musallah shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APGA ta kasa. A tattaunawa da wakilinmu ya ce bai kamata a rika sana siyasa…

 

Alhaji Sadik Ibrahim Musallah shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APGA ta kasa. A tattaunawa da wakilinmu ya ce bai kamata a rika sana siyasa a matsalar tsaron da ake fama da shi a Najeriya ba da kuma halin da Arewa take ciki da sauransu:
Aminiya: Me za ka ce dangane da matsalar tsaro da ake fama da ita a kasar nan?
Sadik Musallah: Da farko halin da kasar nan take ciki a yanzu na matsalar tsaro, akwai babbar damuwa. Domin babbar rigimar da take faruwa na matsalar tsaro da kasar nan take fama da shi, ya sa ake tsoron me zai faru a zaben badi, idan matsalar ta ci gaba ba tare da a magance ta ba. Domin yanzu a kasar nan, gida da daji da kasuwanni da tashoshin mota da ofisoshi kowa na zaune ne cikin tsoro, bai san abin da zai faru shi ba. Don haka babu wani abu da za mu yi a yanzu a Najeriya sai dai addu’a. Sannan mu yi kira ga ’yan siyasa kan maganar saka bama-bamai da maganar sace yara mata ’yan makaranta su fahimci cewa ba abu ne da za a mayar da shi siyasa ba. Ya kamata a taru a kalli wannan al’amari ta fuska daya domin a magance shi. Duk inda dan Najeriya yake a kowace jam’iyya yake ya san idan aka taba dan wani, shi ma ana iya taba nasa. Don haka ya kamata dukkanmu mu hada kanmu mu yi addu’a mu tashi tsaye mu yaki wannan al’amari ta kowane hali.
Aminiya: Wato a ganinka idan tsaro ya ci gaba da tabarbarewa zai yi wuya a gudanar da zaben badi ke nan?
Sadik Musallah: A gaskiya idan abubuwa suka ci gaba da tabarbarewa zaben shekara badi zai zamo da wahala. Domin idan har za a je a sanya bam a kasuwa ko a tashar mota ko a je makarantu a kwashe ’ya’yan mutane ko a je a tare hanya a kashe matafiya. Ta yaya mutum zai fito ya je yakin neman zabe? Ka ga wannan wani babban bala’i ne da kasar ta shiga. Don haka dole ne kowa ya zo a taru mu koma ga Allah mu roke Shi, kan Ya magance mana wadannan rikice-rikice da suke faruwa a kasar nan.
Aminiya: Idan muka dawo ga Arewa wadanne matsaloli ne kake ganin suke damunta a halin yanzu?
Sadik Musallah: Wato matsalar da Arewa take ciki shi ne an so a farraka mu amma har yanzu ba a samu nasara ba. Kuma za mu iya kauce wa wannan makirci da ake ta kulla mana, musamman idan muka manta da maganar bambance-bambancen addini da na kabila. Ka daina ganin kanka a matsayin Kirista ba ruwanka da Musulmi, ni ma na daina ganin kaina a matsayin Musulmi, ba ruwana da Kirista. Mu kalli zaman lafiyar kasarmu, domin idan babu zaman lafiya addinin ma ba zai yiwu ba. Sadoda haka sai mun kalli kanmu a matsayin ’yan Arewa muna kishin Arewar, kafin mu fitar da ita daga halin da take ciki.
Aminiya: Wato a ganinka har yanzu Arewa ba ta karye ba?
Sadik Musallah: Wato idan aka duba a zamatakewar Arewa an so a farraka mu kamar yadda na fada, amma duk da haka Allah bai farraka mu ba. Har yanzu idan ka duba muna zuwa kasuwa daya muna zuwa makarantu daya muna aiki a ofishi daya. Kuma har gobe muna auyatayya a tsakaninmu da juna saboda haka wannan abu da aka kawo mana bakon abu ne da idan muka harere shi da kansa zai gudu. Ya kamata mu gaya wa kanmu gaskiya an haife mu a wuri daya. Kamar mu misali mutanen Jos, za ka samu Birom da Angas da da Bajari da Tibi da Idoma da Bahaushe duk ana haya a gida daya. Don haka ko mun yi fada za mu ji kunya, domin ’ya’yanmu suna makaranta daya ne, za mu hadu a ofis daya da kasuwa daya. Idan ka je Arewa duk asibitoci da makarantu da ma’aikatun gwamnati da otal-otal za ka samu kananan kabilun Arewa suna aiki a wuraren, kuma suna zaune lafiya.
Aminiya:  Ko kana da kira zuwa ga al’ummar kasar nan?
Sadik Musallah: Kirana ga kowa shi ne mu dawo cikin hayyacinmu mu tuna ba mu da wata kasa da ta wuce kasarmu Najeriya. Idan muka bar ta ta wargaje kowa zai sha wuya. Saboda haka mu dawo mu dubi me ya kamata mu yi wa wannan kasa tamu domin ta dore. Mu kyautata dangantakarmu da juna mu taru mu gyara siyasarmu ta koma siyasar gyara kasarmu, ba ta rarraba kai da hada husuma da zubar da jini ba.