✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bafulatani da dan sanda

Wani Bafulatani ne na tafiya a mota da katuwar jaka, sai suka zo shingen ’yan sanda, sai wani dan sanda ya ce, “Jauro mene ne…

Wani Bafulatani ne na tafiya a mota da katuwar jaka, sai suka zo shingen ’yan sanda, sai wani dan sanda ya ce, “Jauro mene ne a cikin jakarka?” Sai Bafulatani ya ce, “Uwarka ce.”
Sai dan sanda ya fusata ya ce,  “Ni kake zagi?” Sai Bafulatani ya ce, “Zaginka na yi, don na ce uwarka ce?” Sai dan sandan ya kai shi wajen babbansu. Aka ce me ya faru sai Bafulatani ya ce tambaya ta ya yi mene ne e cikin jakata, don na ce uwarsa ce ya ce na zage shi. Sai babbansu ya bude jakar sai ga sanda a ciki sai Bafulatani ya ce, “To ba ga shi ba, na ce uwarka ce, ka ce na zage ka, ba sunanka ba ne dan sanda kuma sandar ce a jakata?” Aminu Salisu Dugaji