Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Attahiru Bafarawa da magajinsa, Sanata Aliyu Wamakko sun sasanta bayan wata cacar baki da ta kaure tsakaninsu a baina jama’a.
Masu gaban sun hade ne a wurin ta’aziyar fitaccen malamin addinin Musulunci, Abbas na Malam Babi da ya rasu ranar Talata a Sokoto.
Bafarawa da magoya bayansa sun isa gidan gaisuwar ne ‘yan mintoci bayan isar Wamakko da magoya bayansa.
Wamakko ya so Bafarawa ya mika gaisuwarsu ga iyalan mamacin, amma Bafarawa ya ce sai da Wamakkon ya wakilce su, kuma hakan aka yi.
Bayan sun yi ta’aziyyar, Wamakko ya raka Bafarawa zuwa motarsa inda suka dauki lokaci suna tattaunawa kafin su rabu.
Hakan ya faranta wa mabiya bangarorin biyu rai ganin ba su son su dauki siyasa da gaba, sai dai adawa.
“Mun ji dadin hakan. Ba a fiye ganin hakan ba domin sun dade suna gaba da juna”, inji wani daga cikin magoya bayan ‘ya siyasar.
A Dismabar 2019 ne ‘yan siyasar su biyu suka yi hayaniya a filin jirgi a Sulatan Abubabakar III, bayan Wamakkko ya kira Bafarawa dan cirani.
Kalaman sun yi wa Bafarawa ciwo lamarin da ya sa ya yi watsi da tsohon mataimakin nasa wanda ke kokarin gaida shi a filin jirgin.
“Ka ce ni dan cirani ne a Sokoto, to gaisuwar me za ka yi mini kuma.
“Ubana da kanana haifaffun nan ne, a nan suka rasu kuma zan iya nuna maka makwancinsu.
“Shin kai za ka iya nuna mana kabarin kakanka?”, kamar yadda rahotanni suka ruwaito Bafarwa yana cewa.
Sanata Wamakko bai tanka shi ba, ko da yake wasu rahotanni sun ce bai janye kiran tsohon mai gidan nasa da ya yi dan cirani ba.
“Ba damuwata ba ce in san inda aka binne iyayenka, amma na san kai dan cirani ne a Sokoto, fakat.
“Ko ba kai ne ke kiran mutane da yawa da a nan garin aka binne iyayensu da kakaninsi ‘yan cirani ba”, ya ce wa Bafarawa.
A karshe dai jirgi daya suka hau zuwa Abuja a ranar da suka yi wancan cacar bakin.
Wamakko ya yi wa Bafarawa mataimakin gwamna daga 1999 zuwa 2007 kafin ya ajiye mukamin domin kauce wa tsigewa.
Daga baya ya gaji ya gaji Bafarawan bayan ya kayar da dan takarar Bafarawan, Muhammad Adamu Dingyadi, mataimakin gwamnan da ya gaje shi.