Tsohuwar ministar sufurin jiragen sama, Sanata Stella Oduah tare da wasu mutane takwas sun musanta tuhumar da EFCC ta yi musu ta almundahanar N5 Biliyan.
A ranar Juma’a ne EFCC ta gurfanar da su gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya dake Abuja.
Sauran waɗanda ake tuhuma sun haɗa da Gloria Odita, Nwosu Emmanuel Nnamdi da Chukwuma Irene Chinyere.
Stella Oduah ta sauya sheka zuwa jam’iyyar APC
EFCC ta samu Naira biliyan biyu da rabi a asusun ’yar aikin Stellah Oduah
Akwai kuma kamfanonin Global Offshore and Marine Ltd, Tip Top Global Resources Ltd, Crystal Television Ltd da Sobora International Ltd.
Ana tuhumar Stella Odua da muƙarrabanta ne da karkatar da N5 Biliyan lokacin da take minista a zamanin mulkin shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.