Jami’an tsaro sun cafke tsohon Shugaban Kwamitin Yi wa Harkar Gyaran Fansho na Kasa Kwaskwarima (PRRT), Abdulrasheed Maina a Jamhuriyar Nijer.
Jami’an binciken kwakwaf tare da hadin gwiwar jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ne suka cafke shi.
Majiyarmu mai kusanci da kamen ta ce an yi kama Maina ne sakamakon kawance da kuma hadin gwiwar tsaro da ke tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gurafanar da tsohon shugaban na PRTT ne bisa zarge-zarge 12 na karkatarwa da kuma ta’ammuli da kudaden haram.
A watan Yuni kotu ta bayar da belinsa a kan Naira 500 da wani Sanata da ya tsaya masa, amma daga baya aka yi ta wasan buya da shi kan halartar zaman kotu.
Duk da cewa an kwantar da shi a Asibitin Maitama da ke Abuja, kin halarta zaman kotu daga baya ya sa alkalin kotun, Mai Shari’a Okon Aban ya ba da umarni ranar Litinin da ta gabata a tsare Sanata Ali Ndume da ya tsaya masa a Gidan Yarin Kuje.
Daga baya a ranar Juma’a, alkalin ya ba da izinin sakin Ndume, gabanin sauraron bukatar da Sanata Ndume na kalubalantar kwace gidansa da ke Asokoro ko Naira miliyan 500 da ya jinginar a lokacin belin Maina.