Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya musanta kulla yarjejeniya da Shugaba Bola Tinubu ko Fadar Shugaban Kasa kafin hukuncin Kotun Koli da ya tabbatar da nasarar zabensa.
Wasu dai na zargin cewa yarjejeniya aka kulla a sirrance da gwamnan, shi ya sa Kotun Koli ta soke hukuncin kotunan farko da suka kwace kujerarsa, suka ba wa abokin hamayyansa, Nasir Gawuna na Jam’iyyar APC.
Ana kuma ganin ziyarar Shugaban APC na Kasa, Abdullahi Umar Ganduje, jihar wani bangare ne na tababbatar da yarjejeniyar jam’iyyar da Gwamna Abba.
Akwai kuma wasu takardu da ke yawo a kafofin sada zumunta da suke ikirarin yarjejeniyar ta kunshi sauya shekar Gwamna Abba daga jam’iyyarsa ta NNPP zuwa APC.
- Kungiyar lauyoyi ta kai Ministar Al’adu Hannatu Musawa kotu kan batun NYSC
- Jiragen soji sun kashe ’yan bindiga 30 a Birnin Gwari
Amma a martanin Gwamna Abba, ya bayyana cewa, “takardun da ke yawo ba komai ba ne face soki-burutsu wanda babu gaskiya a cikinsa.”
Sanarwar da kakakinsa, Sanusi Bature ya fitar ta kara da cewa, “Jama’a su yi watsi da wata takardar bogi da ke yawo cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince ya koma APC, ya jingine batun rushe masarautu biyar da ke jihar.
“Gwamna na kara jaddada cewa babu wani mahaluki da ya isa ya yi masa wata barazanar siysa, domin da kuri’un Kanawa ya ci zabe kuma Kotun Koli ta tabbatar da hakan.
“Babu wata yarjejeniya da ya kulla da wani ko wani sharadi da ya amince da shi kafin yanke hukuncin da Kotun Koli ta yi.
“Saboda haka ina kira da jama’a da su yi watsi da wannan shirmen da ’yan adawa suke yadawa.
“Masu fakewa da shugaban kasa kuma su sani cewa duk wani mataki ko alkiblar siyasa da za a dauka a Kano, dole ta kasance bisa doka da kuma karfin ikon da kundin tsarin mulki ya ba wa zababben gwamna.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa Majalisar Dattawan Kano da gwamnan ya kafa, shi da kansa ya ga cewar ya kirkiro ta — ba wani ya sa shi ba — domin lalubo mafita daga matsalolin siyasa da na tattalin arziki domin ci gaban jihar.
Sannan “Duk lokacin da ya nemi ganin shugaban kasa yana ganin sa, kuma abubuwan da suke tattaunawa sun shafi cigaban jihar Kano ne,” in ji sanarwar.