✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Babu wanda aka kashe a harbin Lekki —Gwamnan Legas

Gwamna Sanwo-Olu ya ce babu asarar rai a harbin da sojoji suka yi don kora masu zanga-zanga

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ce ba a samu asarar rai a harbin da jami’an tsaro suka yi a Lekki ranar Talata. 

A ranar ce jami’an tsaro suka yi ta harbi a iska domin tarwatsa masu zanga-zangar EndSARS da suka bijire wa dokar hana fita a Gwamnatin Jihar Legas ta sanya.

“Ni da kaina na ziyarci 10 daga cikin mutanen a Babban Asibitin Jiha, 11 a Asibitin Reddington da kuma mutum hudu a Asibitin Vedic; daga cikinsu mutum biyu na cikin mawuyacin hali, mutum uku kuma an sallame su”, inji shi.

A jawabin da ya yi wa jama’ar jihar bayan ya ziyarci wadanda suka samu raunuka a asibitocin, Sanwo-Olu, ya ce babu wanda aka kashe sakamakon harbin da sojojin suka yi kamar yadda aka yi ta bazawa a shafukan zumunta.

Sanwo-Olu, a jawabin da safiyar Laraba, ya ce jami’an lafiyar jihar, karkashin jagorancin Kwamishinan Lafiya, sun shafe tsawon dare suna karade asibitocin jihar domin bayar da agaji ga wadanda abin ya shafa.