✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu sulhu tsakaninmu da ’yan bindiga – El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya ce gwamnatin jihar ba zata yi sulhu da ‘yan bindiga ba ko kuma yi masu afuwa. Sannan Gwamnan ya…

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya ce gwamnatin jihar ba zata yi sulhu da ‘yan bindiga ba ko kuma yi masu afuwa. Sannan Gwamnan ya bai wa jama’ar jihar hakuri kan tsaron al’umma da ya rataya a wuyan gwamnati.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ziyarci garin Karewa da wasu kauyuka hudu duk a karamar Hukumar Igabi, bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai, inda suka kashe akalla mutum 51 ranar Lahadi.

Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kone gidaje hudu da motoci shida lokacin harin, yayin da jama’ar garin ke ci gaba da neman ’yan uwansu da suka bace.

“Da taimakon hukumomin tsaro ne wasu unguwannin suka tsallake rijiya da baya.”