Fadar Shugaban Kasa ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ke daukar kowanne irin mataki a kashin kansa, ba tare da wani ya tilasta shi ko ya yi masa katsa-landan ba.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban, Malam Garba Shehu, ya fitar a ranar Talata.
- Shugaban Masu Rinjaye da na Marasa Rinjaye a Majalisar Dattijai sun ajiye mukamansu
- Kisan Hanifa: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci
Kazalika, sanarwar ta ce, “Shugaba Buhari na daukar matakansa ne kuma ya aiwatar da su ba tare da wasu da ake wa kallon ’yan hana-ruwa gudu ba sun tsoma masa baki.”
Sanarwar na zuwa ne bayan da ake rade-radi a kafafen yada labarai cewar wasu na yin uwa da makarbiya a gwamnatin Shugaba Buhari.
Hakan ne ma a cewarsu ya sa har ya gaza zabar magajinsa a zaben fid-da gwanin Shugaban Kasa da jam’iyyar APC ta kammala.
Har wa yau, Fadar ta ce irin yadda aka gudanar da zaben na fid-da-gwanin dan takarar Shugaban Kasa a APC, ya nuna cewa Buhari Shugaba ne mai martaba dimokuradiyya duk da cewar shi tsohon soja ne.