Babu wani mai cikakken hankalin da zai sake zaben Jam’iyyar APC a zabe mai zuwa na shekarar 2023 a cewar Sanata Binos Dauda.
Sanata Binos, mai wakiltar Adamawa ta Kudu a karkashin Jam’iyyar PDP ya ce ’yan Najeriya za su yi watsi da APC a zaben 2023 ne saboda yadda jam’iyyar ta jefa su cikin wahalhalu.
- LABARAN AMINIYA: An Tsige Shugaban Jam’iyyar APC Na Adamawa
- Dan takarar Sanatan APC a Jigawa ya riga mu gidan gaskiya
Dan Majalisar Dattijan ya fadi haka ne a yayin da yake raba kayayyakin noma ga manoman Karamar Hukumar Belwa ta Jihar Adamawa.
Binos ya ce alkaluma na nuna cewa zaben da aka yi wa jam’iyyar APC a shekarar 2015 ba karamin kuskure ba ne, ganin halin da jefa ta kasar Najeriya a ciki.
“Ku duba farashin Dala a 2015 da kuma farashinta a yanzu, haka kuma farashin kayayyakin bukatun yau da kullum….
“A bangaren tsaro, shekarar 2015 da yanzu fa? …A ina ne ake zaman lafiya,” in ji dan majalisar.
Ya kuma zargi gwamnatin APC da kawo canji mara amfani ga ’yan kasa da kuma rashin iya mulki da rashin sanin ya kamata.