Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya ce babu wani batun yiwuwar karin farashin man fetur a cikin watan Fabrairu duk da karuwar farashin gangar danyen mai zuwa Dala 60 a kasuwannin duniya.
NNPC ta bakin Janar-Manajnsa na Hulda da Jama’a, Kennie Obateru ya ce rashin kara farashin zai ba da dama gare shi da kungiyoyin kwadago da sauransu masu ruwa da tsaki su kammala tattaunawa game da karbabben tsarin tsayar da farashin fetur ta yadda ba zai cutar da jama’ar Najeriya ba.
- Sojoji 6 sun rasu bayan Boko Haram ta tarwatsa su ta kwashi makamai
- Makarantar Kagara: Atiku ya bukaci a ba sojoji tsaron makarantu
- Matashi ya kashe kansa ta hanyar yanke al’aurarsa a Kano
Kakakin na NNPC ya yi kira ga dillalai da su guji taskance mai don haifar da karancinsa da ganagan, yana mai ba wa jama’ar Najeriya tabbacin cewa a halin yanzu NNPC na da isasshen mai a rumbunsa da zai wadaci kasar na tsawon kwana 40.
Sanarwar ta safiyar Alhamis ta kuma yi kira ga hukumomin kula da bangaren mai da su matsa kaimi don ganowa da kuma hukunta kamfanoni masu taskance mai da gidajen mai da ke kara farashinsa ba bisa ka’ida ba.
A cikin watan Maris na 2020 ne Gwamnatin Tarayya ta sanar da tsame hannunta a bangaren sayar da mai.
Minista a Ma’aikatar Mai, Timipre Sylva ya bayyana cewa yanayin kasuwa ne zai rika alkalanci kan yadda farashin mai zai kasance a kasar.