Babu lallai a ga jinjirin watan Shawwal a ranar Alhamis ta wannan mako da zai nuna karshen wannan wata na Ramadana.
Wata Cibiyar nazarin kimiyyar taurari da ke zama a birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa ce ta bayyana hakan.
- Dan shekara 29 ya doke dan Majalisar Tarayya mai ci a Imo
- Yadda jam’iyyu suka kacaccala kujerun sanatoci a Zaben 2023
Cibiyar ta International Astronomical Center ta ce ba lallai ne a ga watan Shawwal ba a ranar Alhamis, lamarin da ke nufin cewa sai ranar Asabar za a yi sallah Eid Al-Fitr.
A wata sanarwa da cibiyar ta IAC ta fitar a shafinta na Twitter, ta ce ta yi hasashen ne bayan tattara bayanai
Sai dai ta ce hukumomin da aka dora wa alhakin duba wata, su ne kadai za su bayyana ganinsa da kuma ranar da za a yi sallah.
“Ganin jinjirin watan ranar alhamis da Yamma yana da matukar wahala domin yana bukatar na’urar hangen nesa, in ji wani kwararre mai lura da yanayi na musamman.
Cibiyar ta ce ganin jinjirin watan ba zai yiwu ba a ranar Alhamis a ko’ina a galibin kasashen Larabawa, in ban da wasu sassan Yammacin Afirka.
Cibiyar ta ce ba a sa ran ganin watan ko da ta hanyar amfani da na’urar hangen nesa ne. Don haka a ranar Juma’a ne akasarin kasashen musulmi za su sanar da ganin watan Shawwal.
BBC