Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole ya karyata rade-radin da ke yawo cewa yana shirin dawowa a matsayin mai rikon jagorancin jam’iyyar.
Hakan ya biyo bayan zargin da Darekta Janar na Majalisar Gwamnonin Jam’iyyar APC, Salihu Muhammad Lukman ya yi masa na dagula al’amuran kwamitin rikon jam’iyyar domin cimma burinsa na dawowa a matsayin shugaban jam’iyyar.
Alhaji Salihu ya yi zargin hakan ne cikin wata wasika da ya aike wa kwamitin riko na jam’iyyar wanda Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni yake jagoranta.
Oshiomhole ya wanke kansa daha zargin ne a ranar Litinin yayin zantawa da ‘yan jarida a Fadar Shugaban Kasa bayan ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari kan zaben Gwamnan Jihar Edo da ke tafe a ranar 19 ga watan Satumba.
Tsohon Gwamnan Jihar Edon ya ce APC ce za ta yi nasara a zaben jihar, inda ya ce ya nemi Shugaban Kasar ya samar da tsaro mai inganci a yayin gudanarsa.
Ya ce ya bukaci Shugaba Buhari ya tabbatar an gudanar da tsaftataccen zabe cikin nagarta da lumana ta tsari na gaskiya da adalci.
Kazalika ya nemi a hukunta duk wanda aka kama da laifin saba wa doka, ko tayar da zaune tsaye a yayin zaben ba tare da la’akari da jam’iyyar da yake goyon baya ba.