✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu jami’in da za mu yi wa rufa-rufa a badakalar hodar Iblis —NDLEA

Ba m da wani dalili na boye duk wani da bincike ya biyo ta kansa.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyin a Najeriya (NDLEA), ta sha alwashin cewa babu wani jami’inta da za ta yi wa rufa-rufa muddin aka samu hannunsa a binciken da take gudanarwa kan badakalar hodar iblis da ta shafi Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda da aka dakatar, Abba Kyari.

A ranar Litinin ne dai, rundunar ’yan sandan kasar yayin da take sanar da kama Abba Kyarin, ta ce asalin mutanen da aka kama da hodar ta Iblis a Enugu, sun shiga kasar ne da taimakon jami’an hukumar ta NDLEA.

Sai dai a cikin wata sanarwa da hukumar ta NDLEA ta fitar ranar Laraba dauke da sa-hannun kakakinta Femi Babafemi, hukumar ta ce ba ta da wani dalili na boye duk wani da bincike ya biyo ta kansa a muna-munar ta hodar Iblis mai nauyin kilogram 25 wadda DCP Abba Kyari ya jagoranta.

Sanarwar da Babafemi ya fitar yana mayar da martani ne ga wasu bayanai da ke kunshe a cikin sanarwar da rundunar ’yan sandar kasar ta fitar ranar Litinin tana sanar da kama DCP Kyari da wasu jami’anta hudu tare da mika su ga hukumar.

Sanarwar ’yan sandan dai ta yi zargin cewa jami’an ’yan sandan sun yi aikin batar da sahun hodar iblis din ce da hadin bakin wasu jami’an hukumar ta NDLEA da ke filin jirgin sama Enugu.

Sanarwar ta kuma ce mutanen biyu da suka zo da hodar Ibilis din daga Habasha, sun tabbatar da cewa suna irin wannan hulda da jami’an hukumar da ke filin jirgin Akanu Ibiam da ke Enugu tun bara; kuma ko a wannan karon da aka kama su, jami’an hukumar ne suka share musu hanya; kasancewar an turo musu hotonsu da sauran bayanansu kafin su sauka a Enugu.

Don haka rundunar ’yan sandan ta kalubanci hukumar da ita ma ta bayyana sunayensu kuma ta dauki matakin hukunta su.

A kan haka ne NDLEA ta yi martanin cewa ta dukufa wajen amfani da hujjoji wajen gudanar bincikenta kuma duk wani murde gaskiya ba zai sa ta yi rauni ba.

Sanarwar da hukumar NDLEA din ta fitar ta musanta hannun duk wani jami’inta a cikin wannan badakalar tana mai kafa hujja da zantarwar da DCP Kyari ya yi da jami’inta wanda ya tona shi da kuma bayanan daya daga cikin yara Abba Kyarin, ASP Bawa James ya bayar cewa wani mai kwarmata bayanai daga cikin masu safarar kwayoyin ne ya kira su ’yan sanda kai tsaye daga Brazil domin sanar da su cewa ana nan tafe da wannan hodar.

Ta ce a bayanin da ya bayar, ASP James Bawa ya ce wani mai suna IK ne ya kira shi daga Brazil ya kyankyasa masa cewa wasu mutane biyu za su zo Enugu ta jirgin saman kamfanin Ethiopian Airlines da hodar Iblis da zimmar idan aka kama su a kwace hodar a sayar a ba shi na shi kaso.

NDLEA ta kara da cewa hakan ya nuna karara cewa akwai tawagar ta Abba Kyari na da daddiyar alaka da gungun masu safarar kwayoyin da ke Brazil.

Hukumar dai ta ce ta fitar da wannan bayanin ne domin gyara wasu kura-kurai da ke cikin bayanan da aka bayar a baya amma dai ba za ta raga wa duk wanda aka samu da hannu a ciki ba.