✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu dan Boko Haram da za a dauka soja

Fadar Shugaban Kasa ta karyata rahotannin da ke cewa Gwamnatin Tarayya na daukar tubabbun mayakan Boko Haram aikin soja. Kakakin Shugaban Kasa Garba Shehu ya…

Fadar Shugaban Kasa ta karyata rahotannin da ke cewa Gwamnatin Tarayya na daukar tubabbun mayakan Boko Haram aikin soja.

Kakakin Shugaban Kasa Garba Shehu ya ce, “babu ko daya daga cikin ‘yan kungiyar da suka mika wuya da aka yaye da za a dauka aikin soja.

Ya ce, “Babu wanda gwamnati ta taba dauka aikin soja daga cikin ‘yan Boko Haram da aka sauya wa tunani kuma babu wannan shirin”.

A kwanakin baya gwamnati ta yaye tsoffin mayaka 601 da koya musu sana’o’i kar karshin shirin sauya tunaninsu na Operation Save Corridor.

Garba Shehu ya bukaci jama’a da su yi watsi da jita-jitar domin babu gwamantin da ta san abun da take yi da za ta yi hakan.

“Karo na hudu ke nan da ake yaye tubabbun mayakan Boko Haram kuma babu daya daga cikinsu da aka taba dauka soja”, inji shi.

Ya ce gwamnatin Shugaba Buhari na sane da nauyin da ke kanta na kasa da al’umma da kuma wandan rikicin ya yi wa barna.

Ya ce bayanin ya zama wajibi, kasancewar wasu kungiyoyi masu kima da shugaban addini da ‘yan majalisa sun fara yada labarun karya.

An kuma kafa shirin ne bisa koyi da kasashen da suka taba fama da matsalar tare da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai (EU).

“Hukumar kula da ‘yan gudun jihra ta duniya (IOM) ce ke jagorantar shirin [Operation Safe Corridor] a Jihar Gombe.

“Shirin bai shafi ‘yan ta’adda masu tsattauran ra’ayi ba, sai dai kawai wadanda aka tursasa su shiga ko ba su dade da fara da daukar makami ba.

“Kafin yaye tsoffin mayakan sai an tabbatar da tubarsu da zamansu mutanen kirki masu kisin kasa, ta yadda ba za su sake zama hadari ga kansu ko ga wasu ba.

“Don haka akwai hakki a kan al’umma na su karbe su, domin kar a tunzura su su koma abin da suka tuba daga aikatawa”, inji shi.