Har yanzu dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gaza cika alkawuran da ya yi wa ’yan Najeriya a lokacin da yake yakin neman kuri’unsu.
Tsohon Sakataren Hulda da Jama’a na babbar jam’iyyar adawa (PDP), Kola Ologbondiyan ne ya fadi hakan yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a Gidan Talabijin na Channels a ranar Talata.
- Masu garkuwa da mutum 45 a kauyen Kaduna na neman N200m
- ‘Yajin aikin ASUU ya karya harkokin kasuwancinmu’
Ologbondiyan ya ce abin dariya ne idan ana batun cigaban tattalin arzikin Nijeriya karkashin gwamnatin Buhari.
Ya kara da cewa, “Manyan alkawura ukun da Buhari ya yi lokacin yakin neman zabensa, kama daga yaki da rashawa zuwa yaki da ta’addanci da inganta tattalin arzikin kasa, ko daya babu wanda ya cika.
“Rashawa ta samu ’yanci a karkashin gwamnatin APC.
“Dole ne in fada karara ’yan Najeriya na sane da cewa, kaf tarihin Najeriya ba mu taba ganin yadda rashawa ta samu gindin zama kamar yadda muke gani a yau ba.”
Ologbondiyan ya ce a yanzu da ‘yan Najeriya suka zo wuya saboda mulkin Buhari, babu dan APCn da za iya ya fita kan titi ya yi shelar Buhari na aiki saboda gudun abin da ka iya biyo baya.
Ya ce ta kowane fanni Buhari ya gaza, ya kasa cika alkawarin inganta tsaro haka ma batun yaki da rashawa balle kuma fannin tattalin arziki wanda ya fi kowane bangare tabarbarewa.