✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu alakar soyayya tsakanina da Mawaki Akon – Rahama Sadau

Fitacciyar jarumar fina-fina Hausa Rahama Ibrahim Sadau ta bayyana cewa babu wata alaka tsakaninta da mawakin dan asalin kasar Senegal da ke zaune a kasar…

Fitacciyar jarumar fina-fina Hausa Rahama Ibrahim Sadau ta bayyana cewa babu wata alaka tsakaninta da mawakin dan asalin kasar Senegal da ke zaune a kasar Amurka Mista Aliane Damala Bouga wanda aka fi sani da Akon sai dai alaka ta aiki.

Rahma ta bayyana haka ne yayin da take tattaunawa da kafar sadarwa ta Arewa 24, inda ta bayyana cewa tun tana makarantar sakandire take sauraron wakokin mawaki Akon sai dai ba ta taba mafarkin haduwa da shi ba. “tun ina yarinya nake sauraron wakokinsa na san yadda ya shahura, ban taba tunanin zan hadu da shi ba, shi ya sa lokacin da ya aiko min da gayyata don zuwa Amurka na yi murna kwarai da gaske, domin ni a wurina babbar dama ce gare ni da za a kara sanina a duniya.”

Kamar yadda ta sha bayyanawa, Rahma ta musanta zargi da ake yi cewa mawaki Akon ya ja ta zuwa Addinin Kirita in data ce “masu wanann magana ba su san waye Akon ba. Shi fa Musulmi ne wanda yake da mata uku. Kuma Musulmin ma wanda ke riko da addininsa, domin ana gaya min cewa idan watan Ramadan ya kama mawakin ba a ganinsa a cikin mutane sakamkon kebe wa da yake yi don gudanar da ibada.

“Lokacin ina Amurka mun yi maganar zuwa Umara sai yake cewa zai tafi da iyalinsa don haka ya nemi mu tafi tare. Bukatar da na juya wa baya inda na nuna masa cewa idan muka tafi tare mutane za su yada wani abu na daban. Haka ya sa na dawo gida na tafi da ’yan uwana.”

Game da dawowarta harkar fina-finan Hausa jarumar ta bayyana cewa kamfaninta yana nan yana shirya wasu finafinan ban dariya da suka hada da Mati a Zazzau wanda za su fito nan ba da dadewa.

Game da rawar da ta taka a Shirin “Suga” na MTB jarumar ta bayyana cewa ta yi hakan ne don a fadakar da mutanen Arewa a kan abubuwan da suka shafi ci gabansu.

“Da farko lokacin da aka nemi zan fito a shirin na fada musu ba zan yi ba, kasancewar ina kan hanya ta komawa makaranta amma da aka ba ni daftarin shirin gaba daya sai na kira su na sanar

da su amincewata. Saboda akwai abubuwan da ya kamata a ce ana tattaunasu a nan Arewa amma saboda al’adu hakan ba ya yiyuwa, don haka na ga akwai bukatar na wayar wa al’ummata kai ta wannan fannin.”

Jarumar wacce a yanzu ta bude gidan kwalliya, ta bayyana cewa a yanzu ta fi mayar da hankali kan karatunta da take yi a kasar Cyprus da kuma harkar gidan kwalliya da take gudanarwa tare da ’yan uwanta wadanda ake wa lakabi da Sadau Sisters fiye da harkar fim.