Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya ce a shirye yake ya amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi masa.
Obasa wanda ke fuskantar zargin almubazaranci da kuma almundahana ya ce ba shi da wani abin da yake gudun hukumar ta sani, a matsayinsa na dan majalisa da ya san ya kamata.
“Babun abin da zan boye; a matsayinmu na ’yan kasa na gari dun sanda jami’an tsaro masu bincike suka gayyace mu, to hakkinmu ne mu amsa”, inji shi.
Ya kara da cewa, “Hukumar yaki da manyan laifukan tattalin arziki (EFCC) ta aiko min goron gayyata a yau Alhamis.
“Na amsa gayyatar a matsayina na dan kasa kuma dan majalisa da ya san abin da ya dace”.
Ya bayyana haka ne a martaninsa ga gayyatar da hukumar ta yi masa kan zarge-zargen da yake fuskanta.