✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babi na Goma Sha daya: Ziyarar mace ga mijinta a cikin I’itikafinsa:

493. An karbo daga Sa’id dan Ufairu ya ce: “Laisu ya ba ni labari ya ce, Abdurrahman dan Khalid ya ba mu labari daga dan…

493. An karbo daga Sa’id dan Ufairu ya ce: “Laisu ya ba ni labari ya ce, Abdurrahman dan Khalid ya ba mu labari daga dan Shihab daga Aliyu dan Husain cewa: “Hakika Safiya matar Annabi (SAW) ta ba shi labari Hawwala Sanad ya ce, “Abdullahi dan Muhammad ya ba ni labari, ya ce, Hisham ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga Zuhuri daga Aliyu dan Husain cewa: “Annabi (SAW) ya kasance tare da matarsa suka maraita (watse), sai (Annabi) ya ce, wa Safiyya: “Kada ki yi gaggawar tafiya zan raka ki.” Saboda dakinta ya kasance a gidan Usama. Sai Annabi (SAW) ya fita tare da ita, sai wasu mutum biyu daga mutanen Madina suka hadu da shi, sai suka duba zuwa ga Annabi (SAW) sa’an nan suka wuce: Annabi (SAW) ya ce, musu ku zo nan, ku duba da kyau Safiyya ce ’yar Huyayyi ke tare da ni. Sai suka ce, “Tsarki ya tabbata ga Allah! Ya Manzon Allah!” Ya ce, “Lallai Shaidan yana gudanar da mugun tunani ga mutum kamar gudanar jini. Kuma lallai ni, na ji muku tsoron kada Shaidan ya shigar muku da wani mugun zato cikin zukatanku.”

Babi na Goma Sha Biyu: Shin mai I’itikafi zai iya kare kansa daga abin zargi (da magana ko aiki)?
494. An karbo daga Isma’il  dan Abdullahi ya ce: “dan uwana ya ba ni labari daga Sulaiman daga Muhammad dan Abu Atik daga Zuhuri daga Aliyu dan Husain (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Safiyya ta ba shi labari game da haka, Hawwala Sanad ya ce, “Aliyu dan Abdullahi ya ce, Sufiyan ya ba mu labari ya ce, “Na ji Zuhuri yana ba da labari daga Aliyu dan Husaini cewa, “Lallai Safiya (Allah Ya yarda da ita) ta je ga Annabi (SAW) alhali shi yana I’itikafi. Lokacin da ta yi nufin komowa sai ya tafi tare da ita, wani mutumin Madina ya gan su, lokacin da ya kalle su, sai Annabi (SAW) ya kira shi ya ce, “Zo, Safiyya ce tare da ni.” Da yawa Sufiyan ya ce, “Wannan Safiyya ce, lallai Shaidan yana gudanar da mugun nufi ga dan Adam a magudanun jini.” Sai na ce ga Sufiyan da dare ta je masa? Ya ce, “Haka neda dare ta je gare shi.”

Babi na Goma Sha Uku: Wanda ya fita daga I’itikafinsa lokacin safiya:
495. An karbo daga Abdurrahman dan Bishir ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari, daga dan Juraij daga Sulaiman Ahwal kawun dan Abu Najih daga Abu Salmata daga Abu Sa’id -Hawwala Sanad- ya ce, “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Muhammad dan Amru ya ba mu labari daga Abu Salmata daga Abiu Sa’id ya ce, “Ina zaton cewa, lallai dan Labid ya ce, Abu Salmata daga Abu Sa’id (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Mun yi I’itikafi tare da Manzon Allah (SAW) a goma na tsakiyar watan Ramadan. Lokacin da safiyar ashirin ta kasance sai muka rika daukar kayanmu muka je ga Manzon Allah (SAW) sai ya ce, “Wanda ya kasance ya yi I’itikafi to ya koma zuwa ga I’itikafinsa, domin lallai ni, an nuna mini Daren Lailatul kadari a wannan dare. Kuma na gan ni ina sujuda a cikin ruwa da tabo da ya koma ga I’itikafinsa. Ya ce, “Sai sama ta kunsa (lullube) da hadari aka yi mana ruwan sama ina rantsuwa da Wanda Ya aikoshi da gaskiya. Sama ta rufe da giragizai har zuwa karshen wannan yini, kuma Masallaci ya kasance na zuba saboda rufinsa na tankar dabino ne. Hakika na ga alamar ruwa da taba bisa hancinsa da goshinsa.”