Gwamnatin Tarraya ta ayyana ranar Alhamis 30 da kuma Juma’a 31 ga Yuli, 2020 a matsayin ranakun hutun Babbar Sallah.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya sanar da haka a ranar Talata a madadin Gwamnatin Tarayya, tare da taya Musulmi murnar zagayowar sallar ta layya.
Ya kuma ce, “Ina kira ga Musulmi su yi koyi da Annabi Muhammadu (SAW) wajen nuna kauna da jinkai a lokacin nan”.
Sanarwar da ma’aikatar ta fitar a ranar Talata ta taya Musulmi murnar zagayowar sallar ta Layya.
Babbar sakatariya a ma’aikatar harkokin cikin gidan Najeriya, Georgina Ehuriah ce ta sanar da haka a cikin wata sanarwa a ranar Talata.