Al’ummar garin Saminaka da ke Jihar Karamar Hukumar Lere ta Kaduna, sun shiga cikin rudani da tashin hankali, a daren ranar Alhamis din da ta gabata, saboda yadda wata babbar mota ta kwace ta haukan wasu yaran garin su 14.
Rahotanni dai sun ce yaran sun gamu da ajalinsu ne lokacin da suka je aikin roron wake a gona, inda aka rasa rayukan yara, wasu da dama kuma suka samu munanan raunuka.
Shi dai wannan hadarin ya faru ne, a wani kauye da ake kira Bundun Karama a Karamar Hukumar ta Lere.
Wakilinmu ya ganewa idonsa yadda a garin Saminaka, iyayen yara mata da suka tafi wannan aiki na roron wake, suka rika yanke jiki suna faduwa a lokacin da suka sami labarin faruwar wannan hadari, da kuma lokacin da aka shigo da gawarwakin yaran da suka rasu da wadanda suka sami, raunika garin na Saminaka.
Da take yi wa wakilinmu bayani kan yadda wannan hadari ya faru, wata yarinya mai suna Fatima Abdulhadi, wadda tana cikin yaran da suka je roron waken, ta ce wannan hadari ya faru ne da misalin karfe 5:00, bayan sun tashi daga roron a gona.
Ta ce sun kai su 150 da aka dauke su a manyan motoci guda biyu, daga garin Saminaka aka kai su wannan aiki na roron wake, a wannan babbar gona.
“Muna tsaye muna kokarin shiga manyan motoci guda biyu da suka kawo mu, daga garin Saminaka a bakin titi, sai wata babbar mota da ta dauko siminti za ta wuce, sai ta kwace ta yo kanmu.
“A lokacin da motar ta hau kan wasunmu, sai karar fashewar kashi muke ji kawai, wani har kansa ya fita. Shi ne sai mutanen kauyen kusa da wajen, suka zo suka taimaka aka cire gawarwakin wadanda suka rasu da wadanda suka ji rauni.
“Da wannan abu ya faru, sai direban motar ya fito, ya ga abin da ya yi, nan take ya fadi a sume,” inji Fatima.
Da yake zantawa da wakilinmu, wani wanda da rasayaransa uku, mata biyu da namiji daya a hatsarin, Malam Mu’azu Idris, ya ce ya kadu da faruwar hatsarin.
Sai dai ya ce ya mika komai a ga Allah, domin duk abin da ya sami mutum, sai Allah ya so zai same shi.
Daga nan sai ya yi addu’ar Allah ya jikan dukkan yaran da suka rasu.