Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano mai barin gado, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya ce babban kalubalen da ya fuskanta a Kano shi ne yadda ake bayar da belin wadanda suka aikata manyan laifuka bayan an kai su kotu.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a jawabinsa na bankwana a hedikwatar rundunar da ke Bompai.
- Zanga-zangar Kungiyar Kwadago ba za ta shafi sufurin jirage ba —NUATE
- Yadda ’yan daba suka hargitsa unguwar Kurna a Kano
A ranar Laraba ne dai Kwamishinan zai yi ritaya daga aiki, sakamakon cikarsa shekaru 60 da haihuwa.
CP Dikko ya fara aiki a matsayin Kwamishinan ‘yan Sanda daga ranar 19 ga watan Fabrairun 2019.
CP Dikko ya kirayi Gwamnatin Kano da Kotuna a jihar da su duba yiwuwar aiwatar da abinda ya dace dangane da wannan kalubale na bayar da belin wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka.
A cewarsa, “bai kamata a ce wani ya aikata babban laifi ba, kuma a sha wahalar kamo shi amma ya fi karfin doka ba.
Kazalika, CPn ya yi kira ga sauran jami’an rundunar, da su kasance masu bin dokar aikin na dan sanda a duk inda suka tsinci kansu.
Ana iya tuna cewa, a kwanan baya an samu dambarwa a Kano lokacin da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yafe wa wasu mutane da aka kama bisa zarginsu da tayar da hankulan jama’a.