✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Babban Hafsan Soji: Abubwa 3 kan Janar Faruk

Muhimman abubuwa kan sabon Babban Hafsan Sojin Kasa.

A ranar 27 ga Mayu, 2021 aka nada Manjo-Janar Faruk Yahaya a matsayin sabon Babban Hafsan Sojin Kasan Najeriya.

Shugaba Buhari ya nada shi kwana shida da rasuwar magabacinsa, Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru a hatsarin jirgin sama tare da wasu mutum 10, ciki har da janar-janar uku.

Aminiya ta tattaro wasu abubuwan da za su ko sani game da Manjo-Janar Farouk Yahaya:

Tasowarsa:

A haifi Faruk Yahaya ne a ranar 5 ga Janairu, 1966 a garin Sifawa na Karamar Hukumar Bodinga ta Jihar Sakkwato.

A 1985 ya shiga Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin Soji (NDA) a matsayin dan aji na 37.

An yaye shi daga NDA a matsayin Laftanar a ranar 22 ga Satumba, 1990.

Ya yi karatun digirinsa na farko ne a fannin Tarihi, digiri na biyu kuma a kan Harkokin Siyasar Kasashen Duniya da Difilomasiyya.

 

Karin girma:

 1. Kwanan watan karin girman da ya samu kuma su ne:
 2. Laftanar – 27 ga Satumba, 1990
 3. Kyaftin – 27 ga Satumba, 1994
 4. Manjo – 27 ga Satumba, 1998
 5. Laftanar Kanar – 27 ga Satumba, 2003
 6. Kanar – 27 ga Satumba, 2008
 7. Birgediya – 27 ga Satumba, 2013
 8. Manjo-Janar – 27 ga Satumba, 2017.

 

Mukaman da ya rike:

A tsawon lokacin Faruk Yahaya ya rika mukamai daban-daban.

 1. Kafin sabon mukaminsa shi ne Kwamandan Rundunar Operation Hadin Kai mai yaki da kungiyar Boko Haram; Ya kuma taba rike
 2. Babban Kwamandan Rundunar Sojin Kasa ta 1
 3. Kwamandan Rundunar Operation Lafiya Dole mai yaki da Boko Haram
 4. Kwamandan Rundunar Guards Brigade mai tsaron Fadar Shugaban Kasa
 5. Darekta a Kwalejin Hafsoshin Soji ta AFCSC da ke Jaji
 6. Darketa a Hedikwatar Rundunar Sojin Kasa
 7. Shugaban Ma’aikatan Rundunar Operation Pulo Shield da ta yaki ’yan taratsin Neja Delta
 8. Mataimakin Darektan Bincike da Cigaban Rundunar Sojin Kasa
 9. Sakataren Rundunar Soji Kasa
 10. Mataimakin Sakataren Rundunar Sojin Kasa
 11. Kwamandan Rundunar Operation Clean Sweep a yankin Birnin Gwari.

Manjo-Janar Faruk Attahiru ya kuma samu lambobin yabo masu yawa a lokuta daban-daban.