A ranar 27 ga Mayu, 2021 aka nada Manjo-Janar Faruk Yahaya a matsayin sabon Babban Hafsan Sojin Kasan Najeriya.
Shugaba Buhari ya nada shi kwana shida da rasuwar magabacinsa, Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru a hatsarin jirgin sama tare da wasu mutum 10, ciki har da janar-janar uku.
Aminiya ta tattaro wasu abubuwan da za su ko sani game da Manjo-Janar Farouk Yahaya:
Tasowarsa:
A haifi Faruk Yahaya ne a ranar 5 ga Janairu, 1966 a garin Sifawa na Karamar Hukumar Bodinga ta Jihar Sakkwato.
A 1985 ya shiga Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin Soji (NDA) a matsayin dan aji na 37.
An yaye shi daga NDA a matsayin Laftanar a ranar 22 ga Satumba, 1990.
Ya yi karatun digirinsa na farko ne a fannin Tarihi, digiri na biyu kuma a kan Harkokin Siyasar Kasashen Duniya da Difilomasiyya.
Karin girma:
- Kwanan watan karin girman da ya samu kuma su ne:
- Laftanar – 27 ga Satumba, 1990
- Kyaftin – 27 ga Satumba, 1994
- Manjo – 27 ga Satumba, 1998
- Laftanar Kanar – 27 ga Satumba, 2003
- Kanar – 27 ga Satumba, 2008
- Birgediya – 27 ga Satumba, 2013
- Manjo-Janar – 27 ga Satumba, 2017.
Mukaman da ya rike:
A tsawon lokacin Faruk Yahaya ya rika mukamai daban-daban.
- Kafin sabon mukaminsa shi ne Kwamandan Rundunar Operation Hadin Kai mai yaki da kungiyar Boko Haram; Ya kuma taba rike
- Babban Kwamandan Rundunar Sojin Kasa ta 1
- Kwamandan Rundunar Operation Lafiya Dole mai yaki da Boko Haram
- Kwamandan Rundunar Guards Brigade mai tsaron Fadar Shugaban Kasa
- Darekta a Kwalejin Hafsoshin Soji ta AFCSC da ke Jaji
- Darketa a Hedikwatar Rundunar Sojin Kasa
- Shugaban Ma’aikatan Rundunar Operation Pulo Shield da ta yaki ’yan taratsin Neja Delta
- Mataimakin Darektan Bincike da Cigaban Rundunar Sojin Kasa
- Sakataren Rundunar Soji Kasa
- Mataimakin Sakataren Rundunar Sojin Kasa
- Kwamandan Rundunar Operation Clean Sweep a yankin Birnin Gwari.
Manjo-Janar Faruk Attahiru ya kuma samu lambobin yabo masu yawa a lokuta daban-daban.