✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban burina na taimaka wa gajiyayyu a bangaren shari’a – Lauya Jamila Faruk Kaugama

Barista Jamila Faruk Kaugama wata kwararriyar Lauya ce a Jihar Jigawa da ta yi fice wajen taimaka wa mata da marasa karfi musamman a bangaren…

Barista Jamila Faruk Kaugama wata kwararriyar Lauya ce a Jihar Jigawa da ta yi fice wajen taimaka wa mata da marasa karfi musamman a bangaren shari’a.   Hajiya Jamila lauya ce mai tausayi marar son ganin an aikata zalunci,sannan aikinta na lauya bai hana ta wucewa gaba wajen ganin gwamnatin jihar ta taimaka wa marasa karfi ba.  A lokacin mulkin Sule Lamido ita ce mace ta farko da ta tsaya tsayin-daka wajen ganin an fito da wani tsari da za a taimaka wa mata, inda aka tara mata daga jihohin Areawa bakwai, kimanin mutum 500, aka ba su horo a kan yadda za su dogara da kansu, ta  hanyar  ba su tallafin jari a karkashin wani shiri na Jigawa Inbest.  Wakilimmu Umar Akilu Majeri na Jigawa ya samu zantawa da ita, kuma ga yadda tattaunawar ta kaya kamar haka:

Tarihin rayuwa:
Suna Jamila Faruk.   An haife ni a garin Kaugama da ke yankin masarautar Hadeja ta Jihar Jigawa.   Tun ina karama mahaifina ya tafi da ni Kaduna a can na yi makarantar firamare da sakandare daga 1989 zuwa 1995.  Daga nan na koma  Jami ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda na yi digirina na farko a fannin Lauya.  A shekarar 2003 sai kuma na tafi makarantar zama kwararriyar lauya dake Ikko na yi kwas din zama cikakkiyar lauya wato Law school inda na gama a 2004. Na fara aikin lauya a Community Law Centre dake Dutse wato wata cibiya ce ta taimaka wa wadanda ba za su iya daukar lauya ba a gaban alkali domin kare marasa karfi amma yanzu ni lauya ce a Hukumar Zuba Jari ta Jihar Jigawa.   Kuma har yanzu ni lauya ce mai zaman kanta.
Wace gudunmawa kike baiwa matan Jigawa?
Na bada gudunmawa marar iyaka domin a lokacin da nake cibiyar da ke yin sasanci a tsakanin mutane  watau Community Law Center na yi aiki tukuru wajen sasanta tsakanin ma’aurata da masu gonaki da sauransu.
A matsayinki na matar aure hakan bai shafi aikin lauyarki ba?
 Gaskiya ne zaman aure ban samu matsala da maigidana ba domin mijina mutun ne da yas an abinda yake yi kuma yana kishina amma duk da haka bai hana ni yin aikina na lauya ba, domin mijina ya bani goyan baya matuka gaya wajan yadda zan yi aikina ba tare da na samu wata matsala ba.
Yaya batun kalubale ko kin taba fuskantar wata matsala?
 Na sha fuskantar matsaloli amma ina jajircewa saboda a Arewacin Najeriya mata suna fuskantar matsala a wajan aiki saboda karancin mata a aikin gwamnati amma duk da haka tunda na samu goyon bayan mijina  wajen ganin na kai ga nasara akan aikina na jajirce don na taimakawa ’yan uwana mata dake tasowa.
 Me ya ba ki sha’awar shiga aikin lauya a matsayinki na ‘yar arewa inda ba kowa yake da sha’awar shiga aikinba?
Na shiga aikin lauya ne don in taimaka wa ’yan uwana mata wajen kwato masu hakkinsu a kotuna a fagen shari’a domin ana zaluntar mata musamman ma wadanda suke zaune a yankunan karkara.
Wace gudunmawa kike baiwa jama a?
 Na bada gudunmawa mara iyaka musamman ga mata a hanyar aiki musamman a inda nake aiki yanzu na yi wa mata da yawa hanya sun samu jari a Hukumar bada rance ta Jahar Jigawa watau Gigawa Inbest domin ni ce nasa aka kira taron mata 500 wadda aka yi a dakin taro na Sa Ahmadu Bello da ke sabuwar sakatariyar jahar a karkashin ofishinmu na hannun jari watau Jigawa Inbest. A wannan karon an baiwa matan horo akan kasuwanci yadda mata za su dogara da kawunansu aka kuma saka su a hanyar da suka samu ilimin kasuwnci.  Ni ce lauyar wannan cibiya ta Jigawa Inbest, na yi haka ne domin kashi 50 na jama’ar Jigawa suna bukatar a taimaka masu ta fuskar kasuwanci domin su tsaya da kafarsu sakamakon haka ne aka gayyaci mata daga jihohi 7 domin su ganewa idonsu akan me ke faruwa aj ahar a wancan zamanin karkashin shugabana wato Dokta Sagagi.   Aikina na lauya yana matukar taimaka wa jama’a domin abokan mijina ma suna kiran mijina da lauya saboda yana aurena amatsayin matarsa.
Me ke burge ki a rayuwa?
Abinda ya fi burge ni ko ya fi ba ni sha’awa shi ne na ga jama’a suna ci gaba rayuwa cikin walwala da jin dadi ba tare da tsangwama ko kunci ba.
Me ke bata miki rai?
 Ba na son munafunci ko rashin gaskiya.  Ban san na ga ana cutarwa ko danne hakkin jama’a.  Ban son na ga ana zaluntar jama’a.  Hankalina kan yi matukar tashi idan na ga  ana irin wadannan abubuwa.
Wuararen da kika ziyarta?
Na ziyarci kasashe uku da suka hada da Kairo da Ingila da kuma Saudiyy  amma Saudiya ce ta fi burge ni ba domin komai ba sai don kasa ce ta Musulmi kuma akwai addini kuma ko ba komai ina da sha’awar zaman Saudi don in samu damar cigaba da gudanar da addini na cikin walwala da kwanciyar hankali.
Wace irin shiga kika fi so?
Na fi son sanya kaya masu yalwa wayau ina son na ganni kullun a cikin sutura ta mutunci ba irin suturar da za ta rika fito da surorn jikina ba.  Ina kuma bukatar na rika gyara dakina a kullum da jikina kuma na rika yin kwalliya, ba na son kazanta.

Me aka taba yi miki wanda ba za ki taba mantawa da shi ba?
Jama’a sun taimaka min musamman wadanda na yi aiki da su a kan aikina na lauya da inda nake aiki a halin yanzu karkashin ofishin Jigawa Inbest.
Me ya fi baki tausayi?
Abin da ya fi ba ni tausayi shi ne a wata shari’a (case) da na taba kare wani mutun da ake tuhuma agaban kotu bayan na yi bincike mai tsawo sai na gano wanda ake tuhumar ba shi da laifi.   Na tsaya tsayin- daka aka sake shi bayan kotu ta sallame shi amma da alkali ya ce ya sallame shi, yana iya tafiya sai ya fita a guje saboda murna da kidimewa wannan abu ya ba ni tausayi kwarai da gaske.  Ta kai sai da aka kamo shi saboda kamar ya zautu inda na sanya shi a motata na kai shi tasaha na biya masa kudin mota kafin ya wuce zuwa garinsu.   Da na dawo ofis sai da ogana ya yi mini fada a kan me ya sa na dauki mai laifi a motata na kai shi tasha don a zatonsa zai iya cutar da ni amma na shaida masa cewa ai kotu ce ta sallame shi, ba a same shi da wani laifi ba kuma na yi haka ne don na taimaka masa don na ga kamar ya zautu.  Gaskiya wannan abu ya ba ni tausayi matukar gaya.
 Mene ne burinki a rayuwa ?
Ba ni da burin da ya wuce na ga ina taimakawa jama’a a kowane fanni.  Burina shi ne na ga ina taimakawa jihata ta Jigawa don ganin ta bunkasa a kowane fanni.  Kuma burin in taimakawa duk mutumin da na hadu da shi ko na san shi ko ban san shi ba.
Me kika taba yi da jama’a za su rika tunawa da ke?
Na taimaka wajen daidaita ma’aurata.   Na taimaka wajan sasanta rigimar gonaki a tsakanin magada ba tared a cutarwa ba.   Na ga kes din da aka gabatar na yin aure a tsakanin tsofaffi yan shekara 75 da wasu ’yan mata 4 alhalin suna karatun sakandare iyayensu suka cire su daga makaranta amma saboda sun amshi kudi daga wajen wadancan tsofaffi suka sanya dole za su yi musu auren dole amma na yi ruwa na yi tsaki na hana auren.  Wallahi wasu daga cikin tsofaffin da kyar suke tafiya amma wai su ne suke son su auri jikokinsu masu shekara 13  da 14.  Na hana auren bayan an mayar wa da tsofaffin kudin da suka kashe sannan na sa aka mayar da yaran makaranta don su cigaba da karatu.  Kuma sai da suka kammala karatu ne sannan aka yi musu aure. Na yi haka ne don na ceci rayuwar yaran.  To yin haka na san na bar tarihin da ba za a taba manta da ni ba.
Hajiya mun gode da lokacin da kika bani muka yi wannan hira.
Ni ma na gode, Allah Ya bar zumunci.