✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban burina in zama shahararen jarumin fina-finai a duniya – Isa Galwali

Zamu so ka bayyana mana tarihinka  An haifeni a garin Jingir da ke karamar hukumar Bassa a Jihar Filato, amma iyayena dukkansu sun fito daga…

Zamu so ka bayyana mana tarihinka

 An haifeni a garin Jingir da ke karamar hukumar Bassa a Jihar Filato, amma iyayena dukkansu sun fito daga Jihar Kano ne. Aikin kuza ne ya kawo babanmu nan Filato. A wannan gari na Jingir na yi firamare a Islamiyya Primary School. Daga nan na koma Bauchi na yi karamar makarantar sakandire daga nan sai na dawo garin Jos na yi makarantar babbar sakandire. Daga nan na shiga makarantar kimiyya da kere-kere ta Jihar Filato. Bayan da na kammala wannan makaranta sai na kama wannan sana’ ta wakoki da shirya fina- finan  hausa.

Mene ne ya karfafa maka gwiwar shigowa wannan sana’a ta wakoki da shirya fina-finai?

Gaskiyar magana abin da na so na zama tun ina karami shi ne na zama shahararen jarumi mai fitowa a fina-finan hausa. Haka na taso da wannan mafarki nawa. Don haka  kafin na gama makarantar sakandire na fara rubuta fina-finan Hausa ina bai wa wasu masu shirya fina-finan. Ina cikin wannan hali  sai Allah Yasa wani abokina ya bani shawarar cewa ya kamata na fara yin wakokin. Tun daga nan na fara waka a wajen shekara ta 2005.

Wadanne wakoki ne ka fara yi kuma ya zuwa yanzu kayi wakoki kamar guda nawa?

 Wakokin soyayya ne na fara yi, daga nan kuma sai koma  yin wakokin fadakarwa ga al’umma. Kuma wakokin da na fara yi sune  rayuwarmu tana ban tsoro, Mai gaskiya ake rainawa da Waiwaye adon tafiya. Kuma wakar da tafitar dani a duniya aka sanni ita ce Waiwaye adon tafiya.

Ya zuwa yanzu wakoki kamar nawa ka yi?

Gaskiya ban san yawan wakokin da na yi ba. Amma a takaice na yi na siyasa da bukukuwan suna da aure  kamar guda 150.

To yaya aka yi ka tsunduma cikin harkokin fitowa a fina-finan Hausa?

 Na fara fitowa a fina finan Hausa ne kamar yadda na fada saboda sha’awa. Don ina zuwa kallon abin da ake yi daga nan har Allah Ya sa aka fara sanya ni. An fara sanya ni a fim din Azal da na Ali. Ya zuwa yanzu na shirya fina-finai wadanda   suka hada da Gargadi da Kantawaye da ‘Yan doka da Zafin kishi wanda yake kan hanyar fitowa.

Daga lokacin da ka shiga wannan harka zuwa yanzu wadanne irin nasarori ka samu?

Gaskiya mun gode Allah kan nasarorin da na samu a wannan harka, domin na sami nasaraori da dama.  Nasara ta farko da na samu ita ce na bude Studio dina guda biyu a garin Jos haka kuma na bude wani a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna. Kuma ina da yara da dama a wadannan wurare.

Na mallaki  muhalli na yi aure kuma na yi  abin hawa  duk ta dalilin wannan sana’a.

Wadanne irin matsaloli ne ka fuskanta a wannan sana’a?

 Gaskiya na fuskanci matsaloli da dama a wannan sana’a. Ba don hakurin ba da ban kawo wannan lokaci ina yin wannan sana’a ba. Na fara samun matsala tun daga cikin gida a lokacin da na fara wannan sana’a. A lokacin da na fara wannan sana’a ana yi mani kallon wani mahaukaci. Mutanen unguwa da mutanen gari suna yi mani kallon ba zan iya yin waka ba. An rainani ba a dauka ta da mahimmanci. Haka lokacin da nake koyon wannan sana’a na fuskanci matsaloli da dama.

Wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga  abokan sana’arka da kuma sauran masoyanka?

Sakona ga masu wannan sana’a shi ne mu cire kiyayya da hassada domin hassada bata barin mutum ya kai ko’ina. Domin kamar mu masu wannan sana’a muna fama da hassada.