✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan zauna a PSG ba ko nawa za a biya ni — Mbappe

Dan wasa gaba na Faransa, Kylian Mbappe, ya ce ba zai rattaba hannu ba kan duk wani sabon kwataragi da kungiyarsa, Paris Saint Germain ta…

Dan wasa gaba na Faransa, Kylian Mbappe, ya ce ba zai rattaba hannu ba kan duk wani sabon kwataragi da kungiyarsa, Paris Saint Germain ta gabatar masa.

Mbappe mai shekara 22 ya ce ba zai sa hannu a sabuwar kwangilar ba ko da nawa kungiyar da ke buga gasar Ligue 1 za ta biya shi.

Kamfanin Dillancin Labaran wasanni na AS ya ruwaito dan wasan yana cewa, ba shi da wani buri face ganin yana murza leda a Real Madrid ta kasar Spain mai buga gasar La Liga.

Ban ji dadin abin da PSG ta min ba —Mbappe

Paris Saint-Germain ta ki amincewa ta sayar da dan wasan gabanta, Mbappe, ga Real Madrid a lokacin cinikayyar ’yan wasa duk da cewa dan wasan ya nuna sha’awarsa na barin kungiyar.

Amma Mbappe ya hakura tare da ci gaba da zama a PSG duk da cewa burinsa na barin ta bai cika ba, kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da RMC Sport.

“Na sanar da su cewa ina son tafiya, shi ya sa na ki sabunta kwantaragina.

“Na so a ce kungiyar ta samu wasu kudade a cinikayyar da za ta iya amfani da su ta sayi wanda zai maye gurbina.

“Tun tuni na sanar da su cewa ina son tafiya, amma suka ki yin komai a kai. Duk da haka ina fatan dukkaninmu za mu amfana a gaba.

“Gaskiya ban yarda cewa sai ranar karshe ta cinikayyar ’yan wasa ba sannan za a ce za a kammala komai ba.

“Ina nan a kan bakata, na bayyana ra’ayina tun tuni kuma na fada a kan lokaci.

“Amma zan girmama shugabannin wannan kungiya idan ba su so na tafi zan zauna,” a cewar Mbappe.

Madrid tana son sayo Mbappe a Janairu

Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid, Florentino Perez, ya ce akwai yiwuwar kungiyar ta kulla yarjejeniya da Kylian Mbappe a lokacin da za a bude kasuwar hada-hadar ’yan kwallo a watan Janairun badi.

Shi kansa Mbappe ya ce ko a watan Janairu ya tuntubi kungiyarsa ta PSG da bukatar barin kungiyar, abin da yake nuni da cewa dan wasan ya kagara ya bar kungiyar.

Kylian Mbappe ya ce, da kansa ya nemi ya raba gari da PSG a daidai lokacin da Real Madrid take sha’awar sayensa a wannan kaka, duk da dai ya nanata cewa, yana jin dadin zama a birnin Paris.

Real Madrid ta yi tayin dan wasan mai shekara 22 a kan Fam miliyan 137, amma PSG ta yi watsi da tayin, yayin da ta sake yunkurawa, ita ma PSG din ta sake watsi da farashin.

Dan wasan ya ce, yana son komawa Real Madrid domin kauce wa tsarin nan na rabagari da PSG kyauta bayan karewar kwantaraginsa a kaka mai zuwa.

A cewar Mbappe yana son PSG ta samu kudi mai tsoka domin sayo wani kwararren dan wasa da zai maye gurbinsa.

Dan wasan ya ce, matsayarsa a bayyane take game da barin PSG.

Matashin dan wasan ya ci wa PSG kwallo 136 a wasa 182 da ya buga wa kungiyar bayan da ta sayo shi a shekarar 2017 daga Monaco.

Perez ya bayyana fatar cewa a ranar 1 ga Janairu za a yi ta ta kare game da batun kawo Mbappe Santiago Bernabeu.

A wannan kaka ce dai Real Madrid ta yi kokarin sayo Kylian Mbappe daga PSG ta Faransa, amma abin ya faskara, duk da cewa ta sanya wajen Yuro miliyan 170 a kan dan wasan gaban.