A jawabin da yayi wa alummar jihar Kaduna, Gwamnan jiharMalam Nasiru El-Rufa’i ya shaida cewa ba zai yafe wa duk wani da yayi masa kazafi ba, amma wadanda suka zage shi ya yafe masu, sannan yi Allah Ya isa ga malaman da suka zarge shi da hana sallah.
Gwamna Nasiru El-rufa’i ya bayyana haka ne cikin jawabi kai tsaye ta wasu kafofin yada labarai a jihar a ranar Talata, yace ana samun malaman da ke hawa munbari a jihar suna cewa ya hana jama’a yin sallah.
“Ko a Makka ma ba za a yi sallar Idi ba, amma mu a nan malamai sun hau mumbari suna cewa mun hana sallah, alhalin suna sane, don haka Allah ya isa.
“Na yafe wa duk wanda ya zage ni, amma ba zan yafe wa wanda ya yi min kazafi ba.” in ji shi
Nasiru El_rufa’i ya bada tabbacin cewa a ranar sallah, babu mutumin da ya isa ya shiga jihar Kaduna daga jihar Kano kasancewar gwamnatin jihar ta Kano ta amince a gudanar da Sallar Idi da Juma’a, in da ya sha alwashin tsare mashigar Kaduna daga Kano.
“Da kaina zan je hanyar shigowa Kaduna daga Kano na ga mutumin da zai shigo mana, cuta ta riga ta yi katutu a tsakanin mutane sai mu bari su shigo mana da ita? Wannan ba zai yiwu ba” in ji shi.
A baya bayan nan gwamna El-Rufa’i yayi ganawar sirri da wasu malamai da limaman jihar, lamarin da ya sanya al’ummar jihar suka zaci ko za a sami sassauci daga matakan da ya dauka, amma ganawar bata sauya manofofin sa na daukar matakan kare yaduwar annobar COVID-19 a jihar Kaduna ba.