Shugaban Amurka, Joe Biden ya lashi takobin cewa ba zai taba bari kasar Iran ta mallaki makamin Nukiliya ba, matukar yana mulki.
Biden na wadannan kalaman ne lokacin da yake wata tattaunawa da Shugaban Kasar Isra’ila mai barin gado, Reuven Rivlin.
- Ba za mu kara farashin fetur a watan Yuli ba —NNPC
- Hatsarin mota ya lakume rayukan ’yan Najeriya 2,233 a wata 4
“Ina tabbatar maka cewa ba zan taba barin Iran ta mallaki makamin Nukiliya ba a karkashin iko na,” inji Biden gabanin tattaunawarsu a Fadar White House.
Shugaban na Amurka ya kuma shaidawa Reuven wanda zai bar ofis ranar tara ga watan Yulin 2021 cewa kasarsa “za ta ci gaba da zama kadangaren bakin tulu kan duk wani yunkurin Iran na tallafawa ta’addanci.
Kalaman Shugaba Biden na zuwa ne kwana daya bayan ya bada umurnin ayi luguden wuta a kan sansanonin da ’yan tawayen da kasar ta Iran ke goya wa baya suka yi amfani da shi a kan iyakar Iraki da Siriya.
Ana zargin ’yan tawayen da kitsa hare-haren da aka kaiwa dakarun Amurka a kasashen Iraki, inji Biden.
Nan ba da jimawa ba dai ake sa ran ci gaba da tattaunawa don ceto yarjejeniyar shirin Nukiliyar Iran ta shekarar 2015.
Tun bayan janyewar Amurka daga yarjejeniyar a 2018, kasar Iran ta juya baya ga duk wasu dokoki da aka shimfida mata sannan ta ci gaba da aikin inganta ma’adinan Uranium, wanda da shi ne aka kera makaman na Nukiliya da shi.
Wakilan kasashen Jamus da Faransa da Burtaniya da Rasha da China na kokarin shiga tsakani a tattaunawar da ake sa ran yi a tsakanin Amurka da Iran a birnin Vienna na kasar Austria da nufin farfado da yarjejeniyar.
Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump wanda shine ya fice daga yarjejeniyar da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu wadanda suka jima suna sukar yarjejeniyar yanzu dukkansu sun sauka daga mulki, kuma wadanda suka gaje su na duba yiwuwar sauya matsayar kasashensu a kan batun.
Biden dai ya kara jaddada cewa gwamnatinsa zata yi aiki da sabuwar gwamnatin Isra’ila a kan batutuwan kasa da kasa da dama. (dpa/NAN)