✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ba zan daina magana kan shanuna 31 da suka yi

Batan dabo a hannun ’yan sanda ba’ Dattijo Abdullahi Ibrahim, Bafulatani ne da shanunsa 31 da tumakai 2 da kare daya suka yi batan dabo…

Batan dabo a hannun ’yan sanda ba’ Dattijo Abdullahi Ibrahim, Bafulatani ne da shanunsa 31 da tumakai 2 da kare daya suka yi batan dabo a hannun ’yan sanda a Jihar Kaduna. A zantawarsa da Aminiya jim kadan da ’yan sanda suka sake shi bayan sun tsare shi na kwana biyar, ya ce ba zai hakura da maganar shanunsa ba, sai an kwato masa su:

 

Yaya aka yi ’yan sanda suka kama ku?

Habu wato yaro ne ya ce da ni yana son ya dawo gida mu zauna tare, sai na ce masa kafin ya dawo sai mun je an yi magana da bai wa wadanda suke ganin an yi musu laifi ko suka yi mana laifi saboda wannan magana na shanu. A hadu a yafe wa juna kuma a gaban sarkin garinmu aka yi.

Sai sarki ya ce ai ya kamata a dauki wannan magana zuwa wajen hakiminmu da ke Rigachikun ashe wannan magana da muke yi abokan adawarmu su ardo duk saboda wannan maganar shanu da muke yi  sun je sun fada wa ’yan sanda cewa idan mun zo wannan taro a kama mu kawai.

Da muka zo taron kawai sai ga ’yan sanda cikin motoci suka kama mu kuma kamu na wulakanci. Muna da yawa suka kama a wajen amma kowa da gari ya waye  sai ’yan uwansa su je a yi belinsa, sai aka bar ni da Habu.

 

Kana ganin wannan kama ku da aka yi na da alaka da bacewar shanunka?

Kwarai kuwa, ina ganin akwai alaka da shanun da suka bace a wajensu. Kila suna ganin idan aka kama ni aka tsare ai ka ga ke nan zai zama kamar karya nake yi ke nan.

 

Kwana nawa ka yi a hannunsu a tsare?

Kwana biyar na yi a hannunsu amma ba su ko dungure ni ba.

 

Sun fada maka laifinka?

Laifina wai na ce ina da shanu, kai dai magana ce babu kan gado kawai. Kuma wai an ce yarana sun addabi kasa kuma wai suna cewa an sace musu shanu. Alhalin wai shanun ba nasu ba ne  sato su aka yi. Na ce ni shanu nawa ne amma sai suka ce wai karya nake yi.

 

Kuma ka tabbatar shanun naka ne?

Kwarai kuwa shanu nawa ne, kai idan za ka ba ni Alkur’anan da ke Jihar Kaduna baki daya ka ba ni domin in rantse shanu nawa ne.

Wadannan shanu gadonsu na yi shekaru masu yawa daga wajen iyayena saboda haka shanu nawa ne.

 

Yanzu ga shi sun sake ka, yaya maganar shanu?

Ai mu yanzu maganar shanu ku ne kawai za ku taimaka ku kwato mana ’yancinmu. Kuma maganar shanu mu ba za mu fasa yin magana a kansu ba.

 

Wato kana kan bakarka ke nan ta neman a karbo maka shanunka?

Kwarai kuwa.

 

Akwai Kwamishinan Mata Hajiya Hafsat Baba wacce ita ta taimaka wajen karbo ka daga hannun ’yan sanda kuma take kokarin ganin an karbo maka shanunka. Me za ka ce?

Ina mika godiyarmu a kan wannan taimako da take yi mana tare da yi mata fatan Allah Ya ci gaba da kare ta sannan Allah Ya ba ta ikon karbo mana wadannan shanu. Sannan mu a yanzu ita ce muke ganin wacce za mu iya kai kukanmu gare ta a kowane lokaci domin a taimaka mana.

Tun kafin a kama mu dama ni da matata muna da niyyar zuwa wajenta domin yi mata godiya a bisa shirin taimaka mana da ta yi niyyar yi tun a kwanakin baya amma sai ga shi wannan abu ya zo ya faru da ni.

Shi ya sa muke rokonta da ta taimaka mana a kan maganar shanun nan domin duk a kansu ake neman lalata maganar nan.  Idan muka saki maganar shanun nan ka ga yanzu akwai yarona an kashe shi ya bar ni da marayu biyar sannan ga Habu sun kama shi ya bar ni da ’ya’ya.

Ga matata ba ta da lafiya sannan ga shi ba mu da wani isasshen abinci da za mu ci. Idan muka bar maganar shanun nan da me za mu dogara? So ake yarana su ma su tafi su kama sata? Domin su masu karfi ne. Yadda zan daure da talauci in zauna da tsofaffin matana su za su hakura ne? Shi ya sa muke fata a taimaka mana a karbo mana shanun nan domin mu ba za mu yarda ba sai dai idan abin ya fi karfinmu.