Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, bai kamata ‘yan siyasan Najeriya su dauki zaben 2019 a matsayin zaben a mutu ko a yi rai ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne a sakon sabuwar shekara ga ‘yan Najeriya, Shugaba Buhari wanda ke neman wa’adi na biyu a zaben ranar 16 ga Faburairu 2019, wanda za a yi zaben ‘yan takarar shugaban kasa da na majalisar dattawa ya bukaci ‘yan Najeriya su gudanar da sahihin zabe.