Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan.
Yayin jawabi ga Taron Tattaunawa kan Taron Kasa a Fadar Shugaban Kasa, Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Janar Babagana Monguno (mai ritayi) ya yi fatali ta batun sulhu da ’yan bindiga.
- Ya kamata sojoji su bi Boko Haram har maboyarsu —Majalisa
- Hare-haren Nasarawa da Zamfara sun lukume rayuka 30
- Na koya wa Ameachi darasi a siyasa —Wike
Fitaccen malamin Islama, Sheikh Ahmad Abubkar Gumi, wanda kuma tsohon hafsan soja ne na daga cikin masu ba da shawarar tattaunawar sulhu da ’yan bindigar domin a samu zama lafiya.
Amma da yake bayani a Fadar Shugaban Kasa a ranar Laraba, Monguno ya ce yin sulhu zai sa ’yan bindigar su yi zaton cewa gwamanti ta gaza.
Ya ce, “Gwamnati na kokarin shawo kan matsalar tsaro, kuma mun sha fada cewa akwai matakai biyu na magance ta –lallami: tattaunawa, da sauransu.
“Duk da cewa gwamnati ba da adawa da tattaunawa da su, amma tsakanin da Allah dole gwamnati ta yi amfani da karfi a kan wadannan mutane saboda ba su da amana, za ku yi magana da su amma su je su wani na daban kuma su ci gaba da cutar da al’umma.
“Yanzu matakin da gwamnati za ta dauka na magance matsalar shi ne amfani da duk abin da ta mallaka – kayan soji da kuma bayanan sirri wajen kawar da su.
“Idan ana cikin haka wasunsu suka ga sun shirya fitowa a tattauna, to za mu yi hakan da su idan lokacin ya yi, amma a yanzu dai ba za yi ta nanata maganar tattauanwa ba.
“Hankali ma ba zai dauka ba domin tamkar gazawa ce a bangaren gwamnati; na kuma gamsu da maganar Gwamnan Kaduna ta cewa ba abin da zai hana mu gama da su duba da irin abubuwan da muka mallaka.’’