Fadar Shugaban Kasa ta ce ba za a fara amafani da jiragen yaki na Super Tucano wajen yakar ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma ba sai a shekarar 2023.
Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana cewa Najeriya ba za ta iya amfani da jiragen kan ’yan ta’adda a Arewa maso Yamma ba, sai zuwa watan Maris na 2023, wata biyu kafin karewar wa’adin mulkin Shugaba Bubari, duk da cewa ana amfani da jiragen a yaki da ’yan ta’adda a Arewa ta Gabas.
- Gobara ta cinye shugana a kasuwar sansanin alhazai ta Kano
- Yadda aka kama wasu barayin A Daitata Sahu a Kano
“A iya sani na, ba za a fara amfani da su ba har sai watan Maris zuwa Afrilu,” na shekarar 2023, inji Garba Shehu, a hirarsa da gidan talabijin na Trust TV, inda ya bayyana cewa kafin Najeriya ta fara amfani da jiragen na Super Tucano da ta sayo daga Amurka, dole sai ta cika sharadin da aka sanya mata a lokacin sayen su.
Ya ce daga cikin sharudan da Amurka gindaya wa Najeriya, Amurka ba ta yarda a yi amfani da jiragen yakin a wuraren da take kira yankunan fararen hula ba.
Ya ce, “Sojoji suna da kwarewa irin tasu, shugaban kasa na da nasa alhakin.
“Idan ya gama mulkinsa so ne ya koma Kaduna ko Daura ya huta, ba a kai shi Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ba.
“Ya kamata mu bar sojoji su yi amfani da kwarewarsu wajen tunkarar wadannan abubuwa da ke faruwa.
“Idan kana hulda da kasashe irin Amurka, yana da kyau ka bai wa abubuwan da suka shafi al’umma muhimmanci, kamar yadda mu ma yake da muhimmanci a wajenmu.
“Sanin kowa ne, lokacin da suka sayar da Super Tucano ga gwamnatin Najeriya sun sanya sharadi.
“Sharadin bai ba da damar yin amfani da makamai akan farar hula ba, in kuwa aka saba dokar Amurka ba za ta sake sayar muku da makamai ba.
“Kar ku manta an dauki tsawon shekaru ana kin sayar wa Najeriya makamai har sai da Shugaba Buhari ya zo, inda ya kyautata alaka tsakanin Najeriya da Amurka sannan suka amince za su sayar mana.
Sojoji sun kasa amfani da jiragen yaki
“Gaskiya ne da farko rundunar sojin sama ta kasa amfani da jirgin a yankin Arewa maso Yamma.
“Bayan nan kuma, sai da aka dauki lokaci don gano yadda ake sarrafa makaman da jiragen, wadanda makamai ne da ke amfani da fasahar da ba ta kuskure.
“A iya sani na, ko da wannan zai samu a fara amfani da su, sai zuwa watan Maris ko Afrilu,” inji hadimin na shugaban kasa.
Dangane da ceto fasinjojin da aka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, ya ce sojoji na da karfin tarwatsa ’yan bindigar, amma abin da gwamnati take so shi ne bukatar kubutar da mutanen da aka sace a raye.
Ya ce gwamnati ta kashe makudan kudade kan fasahar jiragen sama marasa matuki, kuma ana samun nasara sosai kan lamarin.
Kazalika, ya ce an sake gyara titin jirgin kasan don ci gaba da aiki bayan hari a baya-bayan nan da ’yan bindiga suka kai mishi.
Garba Shehu ya kara da cewa yanzu jirgin kasan zai rika samun rakiyar jirgin yaki, har zuwa lokacin da za a mallaki fasahar da ta dace da jirgin mara matuki.
Ya ce an dakatar da ayyukan jiragen kasa ne domin kada a nuna halin ko in kula ga iyalan wadanda abin ya shafa.
A kan dalilin da gwamnatin take shirin shirya kidayar al’umma a 2023 duk da kalubalen tsaro da ya dabaibaye Najeriya, Garba Shehu ya ce kamata ya yi a gaskata gwamnati kamar yadda ta yi a zaben Anambra duk da matsalar tsaro da jihar ke fuskanta a lokacin.