✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu rage ko kara farashin fetur ba – NNPC

Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Kasa (NNPC), ta bayyana cewa Najeriya ba ta da wani shiri na sarari ko na boye da ta…

Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Kasa (NNPC), ta bayyana cewa Najeriya ba ta da wani shiri na sarari ko na boye da ta ke yi, domin ganin ta rage ko kara farashin man fetur ba a fadin kasar nan a halin yanzu.

A cikin wata sanarwa da shugaban kamfanin na NNPC, Dakta Maikanti Baru ya fitar ta bayyana cewar kamfanin bai da wata aniya ta karin kudin man fetur da dangoginsa ko rage kudin. Sannan ya ce kamfanin yana da isasshen mai da zai wadaci al’ummar kasar nan baki daya, don haka su kauracewa rubibi wajen sanyen man don gudun dagulewar lamura.

Tuni dai Dokta Baru ya bayyana katse wata ziyara da ya ke yi a Birtaniya domin shigewa gaba wajen daidaita al’amura, inda yanzu haka ya ce ya ba da umarnin tunkuda karin man fetur zuwa sassan kasar nan baki daya, don kawo karshen halin da ake ciki. Kazalika Kakakin Hukumar, Nda Ughamadu ya raba wa manema labarai wata takarda a Abuja dake bayyana cewa zancen yiwuwar karin kudin man fetur din ba gaskiya ba ne.

Ya ci gaba da cewa duk da cewa tun a cikin watan Disamba na shekarar 2017 Najeriya take shigo da mai daga kasashen ketare, wannan bai sa ta yi tunanin kara farashin litar man fetur ba, ko kuma sauko da shi kasa.

Sannan sai ya ja hankalin ’yan Najeriya da su guji yada jita-jita da kirkirar labarai na karya don sanya wa jama’a wasuwasi. Haka kuma ya shawarci masu yada irin wannan jita-jitar su daina, domin hakan na iya haifar da karancin fetur a lokacin bukukuwan hutun karshen shekara da Kirsimeti.

Daga nan sai ya kara jaddada albishir da shugaban Hukumar NNPC, Maikanti Baru, inda ya ce a yanzu akwai fetur ajiye, wanda zai iya kai wa kwanaki 37 cur bai kare ba. A kwanan nan ne dai aka yi yayata cewa gwamnatin tarayya na shirin kara kudin man fetir musamman a daidai lokacin da Kirsimeti ke kara kunsatowa, yayin da wasu kuma ke cewa za a rage farashin man ne zuwa kasa ba kari ba.