✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu iya ci gaba da yaki da masu ikirarin jihadi a Mali ba – Faransa

Tuni kasar ta fara rage yawan dakarunta a Mali.

Faransa ta ce “Babu yanayi mai kyau” da za ta iya ci gaba da yakar ’yan bindiga masu ikirarin jihadi a Mali.

Kuma Shugaba Emmanuel Macron ya nemi a sake fasalin dakarun Faransar a yankin na Sahel.

Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean-Yves Le Drian ya ce jasar za ta ci gaba da yakar ’yan bindigar a kasashe
makwabta.

Tuni Faransa ta rage yawan dakarunta a Mali.

A bara ce sojoji suka kwace mulki a Mali, inda aka yi ta samun rikici a
tsakanin gwamnatin da kasashen waje.

A watan Disamba, kasashe 16 – mafi yawansu na Turai – sun yi watsi da
matakin gwamnatin Mali na yin aiki da sojojin haya na Kungiyar Wagner ta kasar Rasha.