✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za a yi facaka ba yayin bikin samun ’yancin kai na bana – Gwamnati

Gwamnati ta ce hatta taron da aka saba yi a Eagle Square, bana babu

Gwamnatin Tarayya ta ce saɓanin yadda aka saba yi a baya, a bana ba za a yi gagarumin biki ba yayin cikar Najeriya shekara 63 da samun ’yancin kai.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis.

Ya ce hatta taron da aka saba yi a dandalin Eagle Square da ke Abuja bana ba za a yi shi ba.

Sakataren ya ce ranar ɗaya ga watan Oktoba ta bana za ta kasance ranar tunani ce ga ’yan kasa domin nazarin makomarta.

George Akume ya bayyana haka ne ga ’yan jaridar da ke Fadar Shugaban Kasa, jim kaɗan bayan kammala taro da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima.

Sai dai bai bayyana ainihin makasudin tattaunawarsu ba, kodayake ya ce a kan abin da ya shafi shirye-shiryen bikin samun ’yancin kan ne.

Ya ce, “Mun shirya tsaf domin yin bukukuwa, amma a bana ba za a yi da aka ba sosai, kuma muna yi wa ’yan Najeriya fatan alheri, daɗi na nan tafe nan ba da jimawa ba.”