Juyin mulki na ci gaba da zama babbar barazana musamman a kasashen Yammacin Afrika.
Ko a baya-bayan nan, kasashe irinsu Mali da Guinea da Burkina Faso, sojojin kasashen sun hambarar da gwamnatocin fara hula ta hanyar yin yujin mulki.
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Gwamnatin Kano Na Dakatar Da Makarantu Masu Zaman Kansu
- Masarautar Bauchi ta tube rawanin Yakubu Dogara
A wata tattaunawa ta musamman da Aminiya, Farfesa Addo Mahamane na Jami’ar Tahoua da ke Jamhuriyar Nijar, ya bayyana abubuwan da ke haifar da juyin mulki a kasashen na Afirka ta Yamma.
Shin me kake ganin na haifar da yawan juyin mulki a kasashen Afirka ta yamma?
Abubuwan da ke kawo juyin mulki a Afirka na da yawa, kuma juyin mulkin ya fi yawa a kasashen Afirka ta yamma tun daga 1963 zuwa yanzu ba a daina juyin mulki ba. Kuma idan ka dauki kasa guda daya kamar Burkina Faso, Nijar ko Najeriya, za ka ga juyin mulki na Najeriya yana da yawa, akwai juyin mulki na 15 ga watan Janairun 1966, wanda a cikinsa juyin mulki uku aka samu a wannan shekara. Ka ga akwai juyin mulki na Janar Murtala, Janar Buhari, Abacha, Babangida.
Idan ka dauki Nijar akwai juyin mulki da yawa, haka nan ma idan ka dauki Burkina Faso, a takaice dai akwai juyin mulki mai tarin yawa da aka yi, musamman a kasashen yammacin Afirka.
Abin da ke yawan kawo juyin mulki ya hada da rashin biyan bukata da Dimokuradiyya ta yi ga al’umma. Da zarar ba a biya bukatun al’umma cikin mulki ba komai ya na iya faruwa, juyin mulki ya na iya faruwa ko jiya ko yau ko kuma gobe. Yakin basasa ya na iya faruwa, ta’addanci ya na iya faruwa, tashin hankali ya na iya faruwa, rabuwar kasa na iya faruwa in dai ba a biya bukatar al’umma ba.
Sannan shan jini wanda turawa mallaka na da, da na yanzu ke yi wa kasashen Afirka idan kishin kasa ya burtsatso cikin zukatan shugabannin Afirka, sai turawan mallaka su sa a musu juyin mulki a kada su, saboda wannan masu kishin kasar suna iya hana su cin ribar da suke ci, tunda tun asali dangantakarsu da kasashen Afrika, su yi wa Afrika shan jinni ne, su ci riba su kwashe dukiya da arzikin da ke Afrika ne don gina kasashensu. Tun daga cinikin bayi zuwa yanzu abin da turawan mallaka ke yi kenan, ba za su bari a zauna lafiya ba, sai dai su yi makarkashiya su samu wasu ‘yan Afrika su yi musu horon soji sannan su taimaka musu su yi juyin mulki ta yadda za su ‘raba guzuma su harbi karsana’.
Salon tafiyar da mulki da shugabannin Afrika ke yi shi ke kawo juyin mulki, inda ka mayar da mulki ‘mutu ka raba takalmin kaza’ wato shugaba ya zame wa mutane dodo sai dai ya kama ya kashe, ya daure ya hallaka kuma babu biyan bukatar al’umma, sannan shugaban ya bi mulki ya kankane daga shi sai ‘ya’yan da ‘yan uwan da abokansa wannan na haifar da juyin mulki.
Wasu na zargin kasar Faransa na da hannu wajen kitsa juyin mulki a wasu kasashen Yammacin Afrika, shin ya gaskiyar lamarin yake?
Babu shakka tarihi ya nuna Faransa, Ingila da sauran kasashen turawan mulkin mallaka na jiya da na yau, suna da hannu wajen juyin mulki da ake yi.
Su suke horar da sojojin, su suke koya musu juyin mulki sannan suke sa musu ra’ayin hambarar da wani saboda suna da ribar da suke ci a kasashen Afrika kan masana’antunsu, kamfanoninsu da sauran ma’adanai da arzikin kasashen, idan ka kalli Nijar da Najeriya sun isa misali. Akwai cin riba ta Dimokuradiyya da suke ci, akwai cin riba ta kasa da kasa da suke yi wajen amfani da kasashen Afirka, wannan bai zama abun tababa ba saboda Faransa na da hannu sosai wajen kitsa juyin mulki.
Bayan samun Dimokuradiyya an yi tunanin juyin mulki zai zo karshe, amma sai ga shi ana ci gaba da samu, shin ina matsalar ta ke?
Dimokuradiyyar da ake yi a kasashen Afirka ba Dimokuradiyya ce da za ta hana juyin mulki ba, saboda ba Dimokuradiyya ce ta Allah da Annabi ba, Dimokuradiyya ce ta turawan mallaka da aka kirkiro wadda ba ta tafiya tare da al’umma, ba ta tafiya da akidar al’umma, ba ta tafiya da matsalolin al’umma, ba ta tafiya da bukatun jama’a. Ga ta nan dai an kirkiro ta an kakaba wa mutane lallai sai sun yi zabe wanda hakan bay a cimma bukatun al’umma.
Idan ka kalli irin yadda ake gudanar da zabe da sakamakon zaben zai nuna maka cewar dimokuradiyyar ba ta da rana, saboda turawan mallakar na ganin irin badakalar da ake yi a lokutan zabe da yadda ake bayyana sakamakon zaben.
Sannnan dimokuradiyyar ta haddasa lalacewar tattalin arzikin kasashe da yawa Afrika, ga ta’addanci wanda a wannan yanayi ne za gas u turawan mulkin mallakar sun shigo da sunan kawo dauki ko tallafi wanda a badili bah aka abun ya ke ba, suna amfani da halin da kasa ke ciki ne don ribatar arzikinta.
Don haka wannan Dimokuradiyya ba za ta hana juyin mulki ba, asali ma sai dai ta haddasa juyin mulkin, saboda ba ta biyan bukatun al’umma ka ga kuwa juyin mulki ba zai kare ba, ta’addancin ba zai kare ba, yakin basasa ba zai kare ba, raba kasa ba zai kare ba kamar a kasa irin Sudan da sauransu.
Shin akwai fargabar samun juyin mulki a wasu kasashe da ke Yammacin Afirka?
Ai tuni juyin mulki ya fantsama ya shafi kowace kasa da ke Afirka musamman idan kasa ta gaza tanadar shugabanci da zai samar wa mutane bege, ko bunkasar tattalin arziki, jagorancin wanda zai sa mutane su samu biyan bukata. Wannan dole ne sai juyin mulki ya shafe su, idan kuma bai shafe sub a yakin basasa ya shafi kasashen, ko ka samu juyin mulkin da yakin basasa a lokaci daya, ko kuma ka ga ta’addanci ya shafe su, ko raba kasa ko ma duka biyun a lokaci daya. Duk wadannan abubuwa dana zayyan tarihi ya gwada yadda suka faru, idan ka dauki Najeriya an yakin basasa an kuma yi juyin mulki, idan ka dauki Nijar an yi tawaye an kuma yi juyin mulki, idan ka dauki Burkina Faso, su ma an yi juyin mulki ana kuma tsaka da yin ta’addanci yanzu tsakanin Burkina Faso, Mali da Nijar, duka abubuwan tare suke tafiya saboda babu biyan bukatar al’umma. Sai an biya bukatar al’umma sannan ita kanta al’ummar za ta zama ‘tsintsiya madaurinki daya’.
Ta yaya za a kawo karshen juyin mulki a kasashen Afirka ta Yamma?
Kawo karshen juyin mulki a kasashen Afirka ya danganta da biyan bukatar al’umma. Biyan bukatar al’umma shi zai sa su zama ‘tsintsiya madaurinki daya’ su yi watsi da juyin mulki, saboda akwai wani amfani da suke ci ta game da yadda ake tafiyar da tsarin shugabancinsu. Kishin kai na iya kawo karshen juyin mulki, saboda ko turawan mallaka sun so sauya ra’ayin mutane ba za su yarda sakamakon suna cin moriya, sun san ribar da suke ci ta yadda ake tafiya da su. In dai Dimokuradiyya na tafiya kan bukatun al’umma komai zai zama daidai, amma idan Dimokuradiyya ta zama ta banza ina mai tabbatar maka ‘ba za a daina juyin mulki a kasashen Afirka ba’.
Tsarin tafiya da mulki ko wane iri ne in dai akwai adalci, rashin nuna bambamci, akida da gaskiya to tabbas babu yadda za a yi ‘kadangare’ ya samu wajen fakewa. Idan ba hanyoyin ‘gaskiya ta fi kwabo’ aka bi ba, babu abin da zai sauya domin kuwa tarihi ne ya ke maimaita kansa.